Main menu

Pages

AMFANIN SABARA WAJEN MAGANCE CUTUKA GOMA GA JIKIN MU

 



Manyan cututtuka guda Tara Zuwa goma da Sabara keyi da yadda za a sarrafata

Sabara da Turanci ana kiranta 'Guiera senegalensis' amma an fi saninta da 'Moshi medicine'. 

Tana fitowa da kanta, ba tare da an shukata ba a guraren yashi da cikin sahara. Tana da koren ganye da 'ya'ya masu kalar yalo da gashi mai laushi ajikinsu. 

Ana iya mafani da Saiwar Sabara da ganyenta da kuma yayanta. 





Ga wasu daga cikin Amfanin da sabara keyi a fannin Kara Lafiya.

 Idan aka samu Sabara, aka cirota, wato da saiwarta da ganyen da yayan da itacenta gaba daya, to tana maganin;


1-  Cutar Kansa 'Cancer'.

     Ana iya daka sabara, a dinga zuba garinta rabin cokali acikin nono,  a sha kullum sau daya,  tsawon kwana goma zuwa sati biyu  don magance cutar kansa. 





2- Kashe Guba. 

    Wanda ya sha magani ba bisa ka'ida ba, 'wato overdose',  in yana gudun maganin ya cutar da shi, ko wanda ya sha guba ko kayan maye,  to zai iya jika sabara a ruwa ya sha, domin tana hana gubar da ke cikin magani ta cutar da mutum. 





3- Gumin dare. 

Wanda yake da matsalar gumin dare, idan yana jika garin Sabara yana sha zai samu waraka,  insha Allahu. 





4- Gudawa. 

    Saiwar Sabara da kuma ganyen Sabara,  suna taimakawa sosai wajen magance matsalar gudawa ga yara da manya. 





5- Basir. 

    Ana tafasa Saiwar Sabara, idan ta dan huce sai a sha,  don magance matsalar basir. 




6- Tsargiya. 

   Mai matsalar fitsari da jini, idan yana shan saiwar Sabara itama tana warkarwa. 




7- Kuraje. 

    Sabara na maganin cututtukan da ke kama fata, kamar kuraje da dai sauransu. 




8- Ni'imar mata. 

   Sabara na taimakawa wajen saukarwa da mata ni'ima. 




9- Shiri da aljanu

An san Sabara kuma an jinjina mata wajen magance matsalolin Aljanu da na sihiri.


Ana iya shan garin Sabara daga cokali daya zuwa kasa a wuni guda,  ba tare da ya cutar da mutum ba.

Comments