Main menu

Pages

YADDA ZAKI SARRAFA MINANNAS DON AMFANA DA SIRRIKAN DA KE CIKINSA

 Sirrikan da ke cikin yin amfani da Minannas

Akwai matan da basu damu da gyaran jikinsuba wanda hakan kuskurene babba domin ita mace 'yar gyarace kigyara ciki da wajenki.
Domin duk macen da batayin gyara tarako mata duniya ne wlh daga yau idan baki gyara to kifara saikinji miji yace zaikara aure kikama hauka


Sirrikan da ke cikin amfani da Minannas

A cikin kayan mata na gargajiya wanda aikinsu yafi karkata wajen ƙara ni'ima bazai taɓa yiwuwa a manta waɗannan ƴaƴan ba, koda yake wasu na aiki da ganyensa kaɗai wajen dakan mata amma dai wannan darasin akan ƴaƴan zamuyi, domin sunfi muhimmanci a wajen mace musamman wajen haɗa garin ciccibi wanda ake dafa jijjiɓin saniya dashi babu yanda zakiyi garin babu ƴaƴansa yayi miki aiki,

Da akwai wani tsumi wanda akeyi da ƴaƴansa da kayan ƙamshi da kananfari, sai a haɗa da sassaƙen bagaruwa da sassaƙen ɓaure a tafasa a bari ruwan yayi tsawon sa'a ɗaya yana jiƙa sannan a tace a zuba masa mazar ƙwaila asha sau biyu a yini ɗaya, tsumin mata ne na masu jego amma ko baki taɓa haifuwa ba ki jarraba,


Adadin yawan ƴaƴan kada ya wuce rabin gwangwani, shima sassaƙen ɓaure da bagaruwa kowanne kada ya wuce cikin gwangwani ɗaya, sai sauran kayan ƙamshi da zaki saka wanda suma gwangwani ɗaya zaiyi, to ruwan dafawa kuwa adadin lita biyu wanda zaki iya kwana huɗu kinashan rabin lita kullum, ita kuma mazar ƙwaila kina buƙatar kifi guda.

Sannan idan kinason kisamu ni'ima emergency zaki iya dafa minanas da danyar citta da kaninfari da Lipton idan yatafasa saiki saka mazarkwaila aciki yanarke kisha shime yana aiki sosai

Sannan ko adafa shayi wato Lipton zaki iya saka minanas aciki dasauran abubuwan dakikeson sakawa.

Comments