Main menu

Pages

HANYOYIN DA ZAKI DON KAUCEWA KARAIRAYEWAR GASHI

 Hanyoyin da Zaki bi don kare kanki daga karairayewa cikin sanyi

Kwalliya ba ta cika sai da kai gyararre. Duk irin jan baki da hodar da za ki shafa, da jagira da zizaren da za ki saka ko ki goga, in har gashin kanki ba a gyare yake ba, to, fa har yanzu da sauran kwalliya” ‘Yan uwana mata, ina me yi muku sallama irin ta addinin musulunci Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

A yau za mu yi duba ne kan hanyoyin warware wata matsala mai cin tuwo a kwaryarmu mu mata. Matsalace da za mu iya kira da karama kuma babbar matsala. Karamar matsala ce in har an san hanyar da za a maganceta, kuma babbar matsala ce in ba a san hanyar da za a bi wajen magancenta ba. Za mu tattauna ne a kan hanyoyin da zamu bi don magance matsalolin bushewar gashin kai.

Mata da dama na fama da wannan matsalar, wasu da zaran sun ji kan su ya bushe, maimakon su fara hada kwabin gashin kai don magance wannan matsalar, sai kawai su dauko man gashi su shafe kansu da shi, wanda yin hakan na iya zama sanadiyar dankarewar gashi, toshe kofofin gashi da hana fitowarsa, musamman idan gashi ya dade ba’a wanke shi ba. Sannan hakan zai iya bawa amosanin kai damar fitowa.

Hanyoyin da za ki bi domin magance bushewar gashin kai sune kamar haka:

1. Kwabin Ayaba

Kayan hadi;

- Zuma cokali daya,

- Nunanniyar Ayaba.


Yadda ake hadawa

Za ki bare bawon Ayaba sai ki markada a injin nika (blender) ta markadu sosai.


Ki zuba zuma cokali daya ki gauraya su su hadu, sannan ki shafa a gashi tun daga karkashin sa har baki.


Ki rufe kan da hular leda (shower cap). Bayan mintuna 15- 20 sai ki wanke kan da sabulun wanke gashi (Shampoo) da na karawa gashi maiko (conditioner).


 2. Kwabin man Zaitun da man Kwakwa.

- Man zaitun

- Man kwakwa


Yadda ake hadawa

Man zaitun za ki hada da Man kwakwa, sai shafa hadin tun daga karkashin gashi

Ki tufke gashin waje daya, sannan ki sa hular leda

Bayan mintuna 15-30 sai ki wanke da sabulun wanke gashi da na karawa gashi maiko
Ga masu laushin gashi yana da kyau su yi amfani da na Ayaba, domin tana kunshe da sinadarin “ potassium” wanda ya ke taimakawa gashin kai wajen sa shi ya yi karfi, yayi kyau.
Sannan yana da kyau don samun kyakkyawan sakamako, ki yi kamar sau biyu a sati. Allah yasa mu dace.

Comments