Main menu

Pages

SIFFOFI DA DABI'U GUDA ASHIRIN NA MACE TAGARI ABIN SON KOWA

 Siffofi da dabi'u guda ashirin (20) na Mace tagari

Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar muhimmanci a zamantakewar iyali. Shi kuwa gida ba ya zama nagartacce sai da mace tagari, wacce take tattare da siffofi abin koyi da za su taimaka mata wajen tafiyar da gidan yadda yakamata.  Don haka ga wadansu daga cikin siffofin da yakamata mu yi nazari a kansu don gane wacece mace tagari? Siffofin sun hada da:


1. Ta kasance mai riko da addini, ba mai sakaci da shi ba.


2. Ta kasance mai gaskiya da rikon amana a kodayaushe.


3. Ta sanya Allah a ranta a duk al’amuranta na yau da kullum


4. Ta zama mai shigar mutunci, misali sanya hijabin da zai rufe mata jikinta yayin da ta fita zuwa unguwa.


5. Ta kasance mai girmama iyaye da ’yan uwa da abokan mijinta.


6. Ta kasance mai yawan kwalliya da ado ga mijinta


7. Ta kasance kwararriya wajen iya girki.


8. Ta kasance mai godiya ga abin da mijinta zai kawo mata, kada ta rika raina abin da mijinta zai kawo mata .


9. Ta kasance mai gaggawar amsa kira yayin da maigida ya kira ta zuwa shimfidarsa.


10. Ta kasance mai kiyaye dukiyarsa da duk wasu kayayyaki da yake amfani da su.


11. Ta kasance mai rufa wa mijinta asiri, ba mai watsa sirrinsa ba.


12. Ta kasance mai ba shi hakuri cikin lalama yayin da ta yi masa laifi.


13. Ta kasance mai nuna farin ciki idan abin farin ciki ya same shi, da nuna bakin ciki idan abin bakin ciki ya same shi.


14. Kada ta yabi mijin wata alhali tana tare da mijinta.


15. Ta kasance mai kwantarwa mijinta hankali yayin da yake cikin damuwa.


16. Kada ta ba wata ko wani dama ya ji sirrinsu  (ita da mijinta).


17. Ta kasance mai kokarin neman ilimi da aiki da shi.


18. Ta kasance mai nisantar abin da ba ya so, ta kuma rika kusantar abin da yake so.


19. Ta kasance mai bin umarnin yi ko bari wajen nuna masa so da kauna a fili, ba a boye ba.


20. Ta kasance mai tausayi, ba mai jawo masa bukatun da ba zai iya biya mata ba. 


Babu shakka da bincike na tsanaki ne ake samun mace mai siffofi nagari abin koyi, gaggawa da kwadayi kuwa a harkar neman aure, babu abin da suke janyowa face da- na- sani, ita kuwa da- na- sani aka ce keya ce.

Comments