Main menu

Pages

BAYANIN DALILAN DA KE JINKIRTA AL'ADA KO HANA TA ZUWA BAKI DAYA

 Matsalar dake kawo jinkirin zuwan Al'adah,ko rashin zuwansa gaba daya

Amenorrhea Idan akace Amenorrhea ana nufin rashin zuwan al'ada na wata daya koma fiye da wata daya. Macen da tarasa period dinta a ƙalla na wata ukku ajere to tana da wannan matsalar ta Amenorrhea.

Amma kamar yarinya yar shekara 15 kuma bata fara al'ada ba to wannan za'a iya cewa tana da matsalar rashin zuwan Al'ada. Mafiyawanci abinda yafi kawo amenorrhea shine juna biyu, sauran abubuwan dake haddasa rashin zuwan Al'ada din sun hada da matsalar data shafi wani sashe na haihuwar mace ko kuma matsalar wata gaɓa wacce ke taimakawa wajen sai ta tsare tsaren tafiyar da matakin hormones, magance wadannan matsalolin shi zai warware matsalar rashin zuwan Al'adar.

Alamomin matsalar

Alamar Matsalar shine rashin xuwan period ya danganta da abun da ya haddasa matsalar rashin zuwan period din wasu matan sukanji wasu Alamomin saboda rashin zuwan period din wanda suka hada da;

1. fitar da madara akan nono

2. Ciccirewarwar gashin kai

3. Ciwon kai

4. Chanjawar gani

5. Ciwon kwankwaso

6. Ciwon fata

7. Yawan gashin fuska


Duk macen da ta jera wata ukku bataga al'adar taba to yana da kyau taga likita ko kuma yarinyar data shekara 15 al'adar ta bata zoba.

Abubuwan dake zama sanadin rashin zuwan Al'adah (Causes)

Rashin zuwan period yana faruwa saboda wasu dalilai da yawa, wasu basu da matsala wasu kuma zasu iya kasancewa matsalolin da wasu magungana ne ke kawo wa ko kuma alamomine na wata matsala ajikin mace.

 - Nafarko akwai rashin zuwan period Wanda ke faruwa bana matsala bane lokacin da yake faruwa na halitta ne kuma Idan lokacin sa ya wuce period din zai dawo;


i. (Pregnancy) wato ɗaukan ciki ga mace Idan mace nada ciki bata al'ada harta haife


ii. (Breast feeding) wato shayarwa wasu matan Idan suna shayarwa basu al'ada


iii. (Menopause) matakine Wanda mace Idan ta kai shi dama ba ita babu period ko haihuwa


Contraceptive wato abubuwan da ake amfani dasu domin hana mace ɗaukan ciki

Wasu matan lokacin da suke amfani da ƙwayoyin maganin hana daukar ciki to period dinsu baya zuwa koda kuwa sun daina sha, yana daukar lokaci kafin tsayayyen al'adar su yadawo da kuma ovulation dinsu.
Maganin hana daukar cikin da aka yi allurar su ko aka dasa su acikin jiki to dukan su suna iya hana zuwan period.


Medications/ kwayoyi na wasu rashin lafiya tabbacin wasu kwayoyin wata rashin lafiya suna iya tsayar da jinin al'ada din mace wadannan magunganan sun ƙunshi:


i. Magungunan da ake amfani dasu wajen magance matsalolin ciwon ƙwaƙwalwa' (Antipsychotics)


ii. Magungunan jinyar cutar sankara (Cancer chemotherapy)


iii. Magungunan ciwan damuwa (Antidepressants)


iv. Magungunan rage karfin jini (Blood pressure drugs)


Wadannan duk suna hana xuwan period Sai kuma yanayin tsarin rayuwar mace yana daga cikin abubuwan dake sanadin rashin xuwan al'ada.


1. Rashin jiki Idan akwai rama sosai ajikin mace yana iya katse hanzarin aikin hormones tayadda al'adar ta zata tsaya


2. Akwai kuma yawan jiki da kuma yawan samun damuwa duk suna tsayarda jinin haila


3. Akwai kuma Hormonal imbalance wanda wasu matsalolin ke haifarwaMisali kamar

Premature menopause mace da ta shiga matakin daina al'adar ta da wuri dama yakan fara ne a matakin shekara 50 to wasu sukan iya shiga tun ma kafin shekara 40.


4. Thyroid malfunction matsalar aikin thyroid rashin aikin ta yadda ya kamata


5. Pituitary tumor da kuma Polycystic ovary syndrome (PCOS).
Matsalolin da suka shafi tsarin sassa na Haihuwar Mace suma suna haddasa rashin zuwan Al'adah

- Misali tabon mahaifa


- Rashin wasu organs din na haihuwa ga mace, wasu lokutan da halittar ke haduwa a cikin ciki ana iya samun naqasun rashin haduwar wasu mahimman sassa na haihuwa yanda ya kamata.


- Kamar Uterus (mahaifa gurin da jaririyake haɓaka a cikin mace)


- Cervix wani (matsatstsen guri a bakin mahaifar mace) ko kuma farji


Wadannan duk idan aka samu naqasu to ana iya samun matsalar rashin xuwan period


 - Cushewar wani 6angare na farji duk yana iya haddasa matsalar rashin xuwan period

Matsalolin da hakan ke iya haofarwa

1. Infertility (rashin haihuwa) saboda Idan mace bata ovulation Sannan kuma bata haila to bata daukar ciki


2. Osteoporosis Idan rashin xuwan period din ki a dalilin karancin estrogen ne to kina cikin hadarin kamuwa da matsalar Osteoporosis wato raunin kashi wato rashin kwarin kashi.

Comments