Main menu

Pages

ABUBUWAN DAKE HADDASA CUTAR BUGAWAR JINI, KO BUGAWAN ZUCIYA

 

Abubuwan da suke haddasa bugun Jini, ko bugawar Zuciya a likitance.

Farfesa Balarabe Sani Garko, kwararren likita ne a fannin cutukan da suka shafi zuciya da hawan jinni da makamantansu a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello, Shika Zaria, ya yi wa BBC Karin haske a kan ita kanta cutar.
Kwararren likitan ya ce, idan aka ce mutum ya gamu da lalurar bugun jinni to ya samu matsala ne da hanyoyin da jini ke bi a jikin dan adam da kuma bangaren kwakwalwa.


Wata kila a samu hanyar jini ta toshe ko kuma hanyar jini ta fashe jini ya hadu da wani abin, wannan shi ake cewa bugun jinni wato a turance stoke, in ji likitan.

2022

Kwararren likitan ya ce, akwai abubuwan da ke janyo  ita wannan cuta kamar idan zuciya ta na buga jini ya tafi da karfi, wato kama hawan jini ke nan.


Ya ce,” Baya ga hawan jini da ke janyo wannan cuta, akwai kuma ciwon siga, da a turance ake cewa Diabetes, shi ma yana janyo wannan cuta ta bugun jini.”


Likitan ya ce, idan wasu abubuwa ma suka yi wa mutum yawa a jikinsa kamar kitse, su kan daskare su toshe hanyoyin jini wanda hakan zai jawo matsalar gamuwa da bugun jini.
Farfesa Balarabe Sani Garko, ya ce akwai matakan da ya kamata a dauka don kaucewa kamuwa da cutar bugun jinni kamar kaucewa duk wani abin da aka san zai iya janyo toshewar hanyoyin jini sai kula da su.


Ya ce, kamar misali idan mutum na da lalurar hawan jini, yakamata ya rinka zuwa asibiti ana duba shi da kuma auna shi, haka smai lalurar ciwon siga ma, dole a kula.
Kwararren likitan ya ce, yakamata mutane ma su rinka zuwa asibiti ana duba yawan maiko ko kitsen da ke jikinsu wato Cholestrol don kaucewa kamuwa da cutar bugun jini.


Likitan ya ce, baya ga duba irin wadannan cutuka, yana da kyau mutane su rinka zuwa ana duba kwakwalwarsu da koda dama sauran abubuwa da suka kamata a rinka ana duba lafiyarsu akai-akai a asibiti.

Farfesa Balarabe Garko, ya ce, ita cutar bugun jini ba wai kawai masu shekaru da yawa ta ke kamawa ba, yaro ko matashi ma na iya kamuwa da ita, a don haka dole mutane su kiyaye

Comments