Main menu

Pages

YANDA AKE HADA HADADDUN TSUMI DOMIN UWARGIDA DA AMARYA

 Hadadden Tsumi na Musamman domin Uwargida Da Amarya kadai. 

Wata fa'ida ce wacce ya kamata kafin na fada, kowacce mace da zata yi amfani da ita ta bani wani tukwici amma saboda maigida na bar muku shi kyauta. 


Macen dake su ta rikita maigida to ga hanya mai sauki da zaki tsuma kanki, ke ko mota kike so indai kikai wannan hadi tofa kin samu,amma fa idan an samu mota kar a manta dani. Hanyar kuwa itace. 


 Zaki nemi:

 1. Dabino 

 2. Kwakwa (coconut) 

 3. Nonon Rakumi 

 4. Zuma 


 Yadda Zaki hada

 Da farko zaki cire kwallon dake cikin dabino,sai ki kawo kawar ki bayan kin bare bawon ta ki samu ruwa kadan ki zuba a kai kiyi blending nasu.


 bayan kin gama sai ki kawo zuma kamar rabin kofi nonon Rakumi kamar kofi daya ki hada da kwakwar nan da kika hada da dabino ki hafe da zuma da nonon Rakumin waje daya. 

 Ki rika sha kadan kadan kamar tsawon kwana 7 zaki bada labari.
Hadin Zuma:

1. Zuma 

2. Garin habbatus Sauda 

3. Man zaitun

 Karin ni’ima damotso sha’awa zaki sami zuma mai kyau ki zuba garin habbatus-sauda da man zaitun ki juye su guri guda sai ki dinga sha babban cokali biyu da safe da kuma yamma.

Hadin Danyen Kwa: 

Yana karawa mace kuzari ba tareda ta gajiya ba wajen jima’I kuma yana karawa mace ni’ima da sha’awa.


1. lipton 

2. Danyen kwai 

3. Zuma 


Ajika lipton da ruwa kadan har sai yayi baki, sai ki fasa kwai ki hada shi, sai ki zuba cikin ruwan lipton kina iya zuba madara peak sai ki zuba zuma ki dinga sha.

Hadin Sassaken Baure:

Zaki iya yin shayin kara karfin sha'awa da ni ima yanda zakiyi shine kisamu sassaken baure ki dakashi sai ki daka kanunfari ki hada da lefton kinasha zakiyi mamaki. SHARE TO OTHERS

Comments