Yadda Ake ingantacce hadin Ridi don Karin Ni'ima ga Mace
Anso miji da mata su ringa amfani da wannan hadin domin Karin ni’ima yana kuma sa koda yaushe ta dinka bukatar mijinta kusa da ita.
_Garin Ridi: Za a Samu kankana akasa kashi 3, za’a dauki kashi daya daga cikin 3, sai a hadasu a zuba a cikin blander a markade, sai a zuba garin ridi a ciki, a zuba madara da zuma ki zuba wa angonki cikin kofi kisha ya sha. Wannan hadin yana kara ni’ima sosai da sosai.
Si Hadi na biyu Kuma zaki samu wadannan abubuwan kamar haka;
1.Ruwan Kwakwa
2. madaran peak
3. Zuma
4. Ridi
Za ki hade su wuri guda ki ringa sha yana kara ni’ima sosai da sosai.
Hadin Ridi (Karin ni’ima da kuzari) anso miji da mata su ringa sha domin motsa sha’awa._
1. Kanunfari
2. Zuma
3. Garin Ridi
4. Nonon shanu Mara tsami
Ki dafa kanunfari da ruwan zafi idan ya dauko nuna (dahuwa) sai ki sauke ki sami garin ridi da nonon shanu mara tsami, ki hade guri daya ki gauraye. Ki saka a firiji ko ki saka kankara idan yayi sanyi sai ki sha. Wannan hadin idan kinyi sai kuma bayan mako daya za,a kuma yi
Comments
Post a Comment