Main menu

Pages

IRE IREN ABINCIN DA YA KAMATA MA'AURATA SU DAINA CIN DON INGANTA LAFIYARSU

 
Nau'ikan abincin da ya kamata ma'aurata su kauracewa cinsu don suna daqushe sha'awa.


Ba shakka akwai kyakkyawar alaka tsakanin abincin da mu ke ci da kuma lafiyarmu, haka nan lafiyarmu na da kyakkyawar alaka da yadda sha'awarmu ke motsawa kuma mu ke iya gamsar da iyalinmu.


Yana da kyau mutum ya san yadda zai tsara abincin da yake ci yau da kullum, sannan ya nacewa cin abinci mai gina jiki don samarwa da jikinsa cikakkiya lafiya da kuzari har ya iya biyan bukatar matan aurensa. Hakanan cin abinci barkatai kuma wanda ba ya kunshe da sanadarai masu gina jiki, ko kuma yana dauke da wasu sanadarai masu illa ga jiki to lalle zai haddasawa jikin illa kuma ya hanawa mai gida katabus.

Mai karatu zai ga ko da yaushe mun nace da zancen abinci game da zamantakewar aure, ba wani abu yasa hakan ba sai dai saboda irin bincike da aka gudanar kuma har yanzu ake kan gudanarwa akan alakar lafiyar jikinmu da abincin da mu ke ci yau da kullum.


Tun da farko dai muna kyautata zaton mai karatu ya kwan da sanin cewa, daga abincin da mu ke ci ne, mu ke samun ingantacciyar lafiya da kuzari. Kuma rashin abincin mai inganci ya kan nakasa mutum har ka ji ana cewa yunwa ta huda shi.

Bayan wadannan dalilai da mu ka zana a sama, masana a wannan zamani sun fi karkata ga tsara cin abinci da kuma cin mai gina jiki saboda shi ba shi da wata matsala ga jikinmu sabanin kwayoyin sa kuzarin jima'i da ke haifar da illoli masu yawa ga jikin dan adam.

Don haka dole ne mu fahimci cewa a cikin abincin da muke ci akwai wadanda ke rage sha'awa ga ma'aurata sakamakon canjin da su ke haifarwa jiki. Misali duk abinci mai maiko da yawa, ko mai yawan gishiri, ko masu zaki da yawa, kan dakushe sha'awa ga ma'aurata.


Ganin amfanin wannan mas'ala mu ka ga dacewar zayyana ire-iren wadannan abinci don ma'aurata su nisance su.
1. Abincin Da Aka Sarrafa.

Abin nufi anan shine ire-iren abincin da ake sarrafawa a kanfuna a zuba su a mazubi dabam-dabam kamar leda, kwali buhu da sauran su.


Yayinda ake sarrafa wadannan nau'in abinci ana matukar rage masa sanadaran da ke da alfanu ga jikin mutum, wannan kuwa ya hada da sanadaran da ke ingiza sha'awa da kuma kara kuzarin namiji, da kuma wadanda ke karawa mace sha'awa da ni'ima.

Binciken da masana suka gudanar akan alkama ya nuna cewa idan aka sarrafa ta zuwa filawa, to an yi hasarar wani sanadari na "zinc" da take kunshe da shi da misalin kashi uku bisa hudu. Wannan na nuna cewa idan ba'a sarrafa ta da na'ura ba ta fi amfani a jikin dan-adam.


Hakan na nuni da cewa yawaita amfanin da irin wannan nau'i na abinci lalle zai iya tasiri game da kuzari da sha'awar amarya da ango.


2. Sukari.(ko duk wani abu mai zaqi)

Shi sukari da dangogin abinci masu yawan zaki ba kawai suna rage karfin sha'awa ba ne kadai, a'a harma da rage karfin mazakutar namiji.


Wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa yawan shan sukari na rage yawan sanadarin halitta na "testosterone" a jikin mutum shi kuma karancin wannan sanadarin kan shafi jima'in mutum kwarai da gaske.


Saboda wannan dalili ne yasa ake bada shawara ga ma'aurata su guji shan sukari da ya wuce kima.

3. Maiko

Yawaita cin abubuwa masu maiko kamar kitse na haifar da wani maiko na cikin jini wanda ya ke toshe hanyoyin jini, ita kuma gudanar jini na da kyakkyawar alaka matukar gaske da jima'i.


Mun fada a makalarmu mai taken nau'ikan abinci masu karawa namiji sha'awa da kuzari yayin jima'i cewa yayinda ma'aurata su ka himmatu da yin jima'i jini ne ke kwarara zuwa al'aurarsu musamman namijin don hakan ne ke haifar masa da mikewar azzakarinsa.


Kun ga kenan duk abin da zai kawo matsewar hanyar jini to ba shakka zai haifar da matsala ga faruwar jima'i mai gamsarwa.

4. Abincin Gwangwani.

Nau'in abincin da ake sarrafawa sannan a zuba shi a gwangwani na haifar da matsala ga ma'aurata ta fuskar sha'awa da gamsar da juna.


Ba komai ke haddasa hakan ba, sai don bayan rage masa sanadarai masu muhimmanci wajen gina jiki, hakanan ana sanya wasu sanadarai don gudun ya lalace.


Wadannan dalilai yasa ake baiwa ma'aurata shawarar rage cin ire-iren wadannan abinci.

.

5. Kayan Sha Na Gwangwani.

Wadannan nau'inkan abinci na da kamanceceniya da sukari, sai dai inda su ka sha bambam shine, su wadannan an sarrafa su, sannan kuma aka sa musu sanadaran da za su hana su lalacewa, kamar dai kayan abinci da aka sarrafa aka sa cikin gwangwani.


6. Kayan Toye-toye.

Su wadanan sun hada da irin su cincin, fanke, alkubus, da dai sauran nau'ikan wannan abinci. Su wadannan nau'ikan abinci suna hana jikinmu samun damar ribanyar wasu sanadaran halitta da ke da matukar muhimmanci ga ma'aurata yayin jima'i "testosterone" da kuma "estrogen" da turanci.


Bincike ya nuna a duk lokacin da aka ce wadannan sanadaran halitta sun yi kasa, to ba shakka hakan kan shafi yanayin sha'awa da kuma gamsar da juna.

7. Tabar Wiwi.

Karanta: Gani ya kori ji. kalli hotun illolin da shaye shayen miyagun kwayoyi ke haifarwa


Ita dai mun sani haramun ce a addininmu na musulunci, hakan dokar kasa bata yarda ai safara ko shanta ba, amma duk da haka wasu kan zuke ta ko a boye ne.


Bincike da aka gudanar akan ta ya nuna cewa tabar wiwi na sanya sanadarin nan na "testosterone" da muka ambata yin kasa sosai har na tsawon awa 24.
 Tabdijan, to mai karatu ai ko ba'a fada ba kasan wannan taba lalle za ta nakasa mai shanta, nakasawa kuma mai barazana ga dankon soyayyar aure harma da haihuwa.


Muna fatan ma'aurata za su nisanci wadannan nau'ikan abinci don samun ingantacciyar rayuwar aure mai cike da nishadi, kaunar juna da kuma zamantakewa abar kwatance. Allah Ya sa mu dace amin.

Comments