Main menu

Pages

YADDA AKE HADA MADARAR WAKEN SOYA TA RUWA DON SHAN TEA

 Yadda Zaki hada Madarar waken soya ta Ruwa don Shan tea


Ki siyo waken soya ki cire mishi datti saiki surfa kamar yanda ake surfen wake saiki wanke ki cire dusar,Saiki jika ya kumbura saiki markada a blender ko Kuma idan a inji ne kice su wanke da kyau kada su Sanya miki wani abu a ciki idan an kawo ki tace da kauri ki daurashi a wuta ya dahu sosai zaki ga ya kara kauri saiki sauke kisa flavour ki Sanya a fridge idan Kuma baki da fridge zaki iya duk lokacin da zaki sha ki dafa sabo,

Idan zakiyi amfani dashi kiyi warming kisa citta da lipton bayan ya dahu ki tace kisa Milo da suga,


Ina tabbatar miki wannan tea din yafi na kowacce irin madara da kike Siya a kasuwa test din daban ne.

Comments