Main menu

Pages

ILLAR SAYEN SABUWAR WAYA KO TSOHUWA (SECOND HAND) A WANNAN LOKACIN

 Illar sayen sabuwar waya ko tsohuwa (second hand) a wannan lokacin.

Dalilin wannan rubutu shine, domin hankaltarwa da Ilimantarwa akan illar siyan waya sabuwa ko second hand.


A yau damfara ta hanyar siyan sabuwar waya ko kuma second hand ta zama tamkar ruwan dare wanda hakan yanzu yana faruwa akan wasu.

Da farko akwai Wasu Kampanoni wandanda suke bawa mutum bashin waya, irin su PAMPLAY da EASYBUY ta hanyar sakawa mutum "Security Plugin"


ESSYBUY DA PALMPLAY Bankuna ne da ake anfani dasu wajen sakawa da cirewar kuɗi da kuma biyan katin wuta, ruwa, waya, dasauransu. Wadannan bankuna suna bawa mutum bashin waya, ba tare da kuɗin ruwa ba, ta hanyar sakawa mutum "Security Plugin" wannan Plugin ɗin aikinsa shine : tsayarwa ko dakatar da wayarka daga yin aiki ko kuma kulleta, ko turama mutanen da kaƙe da lambobinsu saƙo cewa kaci bashi kuma kaki biya.

Shin Tayaya Ake Damfara Ta Wannan Hanyar ?

~ Yanzu Madamfara sun ganewa wannan hanyar ta cin bashi a cikin "Easybuy ko Palmplay" idan sun siya wayar bashi, ana saka masu wannan "Security Plugin" ɗin a cikin ta, dama ba sunci bashin bane don su biya ba, sun siya ne kawai don su cutar ta Jama'a wanda basu ji ba basu gani ba. Zasu siyar maka da wayar domin kar su biya bashin kai, kai kuma da baka sani ba idan ka siya kai zai shafa, sai a kula.


Comments