Main menu

Pages

TOGA! RIKICI YA BALLE TSAKANIN DANGOTE DA GWAMNAN JIHAR KOGI




Rikici yayi tsamari tsakanin Ɗangote da Gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello

 Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya umarci shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya gaggauta rufe kamfanin dake Obajana cikin awa 48 ko kuma gwamnatin jihar ta ɗauki mataki a kai.




Gwamna Bello ya ce ya bada wannan umarni ne bayan Ɗangote ya ki amsa gayyatar da majalisar jihar Kogi ta yi masa da ya bayyana gaban majalisar domin amsa tambayoyi game da halascin zaman kamfanin a jihar Kogi.




” Tun da Ɗangote ya ki am sa gayyatar kwamitin majalisar jihar Kogi, ni gwamna Yahaya Bello zan hukunta shi, Ɗangote bai fi karfina da mutanen jihar Kogi ba.




” Saboda haka na bashi awa 48 ya rufe kamfanin, a daina aiki a cikin sa. Wannan shine umar nina kuma dole ya bi, idan ba haka ba zai gamu da abinda ba haka ba.




Martanin Ɗangote ga Gwamnatin Kogi

Gamayyar Rukunin Kamfanonin Ɗangote Industries Ltd, ya fitar da kakkausan raddi ga Gwamnatin Jihar Kogi dangane da dambarwar da ta haddasa rufe Masana’antar Siminti ta Ɗangote Cement da ke Obajana, Jihar Kogi.




Kakakin Yaɗa Labaran DIL na rukunin masana’antun Dangote mai suna Anthony Chiejina, ya fitar da raddin a ranar Laraba, inda a cikin dogon bayanin da ya yi dalla-dalla, ya ce Gwamnatin Jihar Kogi ba ta da sauran haƙƙi ko na buhun siminti cikin kamfanin a matsayin hannun jari.




“Gwamnatin Jihar Kogi ba ta sauran ko sisi a matsayin kuɗin ruwa ko hannun jari a cikin Dangote Cement PLC da ke Obajana.




“Dangote Cement tun da ya fara aiki a 2007, bayan ya sayi kamfanin daga Obajana Cement a hannun Jihar Kogi cikin 2002, bai daina biyan haraji ba. Kuma ya na biyan kuɗaɗen duk wani nau’in haraji da sauran caje-caje.




“Abin takaici ne yadda Gwamnatin Kogi ta yi amfani da ƙarfin gwamnati ta sa aka kulle masana’antar. Idon ta ya rufe, ta kasa yin la’akari da cewa akwai ma’aikata fiye da 22,000 masu aiki a masana’antar. Kuma da ita su ka dogara wajen ciyar da iyalin su.





“Ya zama dole mu fito mu yi wa jama’a bayani, ganin yadda dubban ma’aikata, ‘yan kwangila, masu hannayen jari a ciki, dillalai da waɗanda mu ke hada-hadar kuɗaɗe da su da kuma sauran masu ruwa da tsaki su ka damu da dambarwar da ke faruwa.


“Rufe masana’antar ya jefa ƙasar nan cikin wata matsalar tattalin arziki, amma Gwamnantin Kogi ba ta yi la’akari da hakan ba.




“Ya kamata jama’a su san cewa a yarjejeniyar cinikin Obajana Cement da aka yi cikin 2002 inda Dangote Cement ya saye shi, kuma yarjejeniyar kafa Ɗangote Cement ta tabbatar da cewa ƙasar da aka gina masana’antar, mallakin Ɗangote Cement ce, injina da sauran kayan aiki ma duk mallakin sa ne.




“Kuma albarkatun ƙarƙashin ƙasa da ke wurin su ma an samu haƙƙin mallakar su ne daga Gwamnatin Tarayya a bisa ƙa’idar dama ko izni na wasu ƙayyadaddun shekarun da gwamnati ke sabuntawa bayan wasu shekaru.




“DIL ya samu haƙƙin mallakar wurin cikin 2003, shekara ɗaya bayan yin cinikin Obajana Cement.


“An ba mu satifiket na haƙƙin mallaka iri uku, bayan mun biya dukkan kuɗaɗen da doka ta tanadar, kuma mun biya dukkan kuɗaɗen diyya ga al’umma mazauna yankin ko masu gonakin.”




Cheijina ya ce a kwantar da hankali, domin tuni kamfanin Dangote Cement da DIL sun kai ƙorafin su ga Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin da abin ya rataya a wuyan su.




Asalin Dambarwar:

Kamfanin Dangote Cement ya ce ‘yan iska da ‘yan bijilanten Gwamantin Kogi sun raunata ma’aikatan kamfanin.


Kamfanin Simintin Ɗangote ya bayyana cewa gungun wasu ‘yan iska da ‘yan bijilanten da Gwamnatin Jihar Kogi ta tura domin su kulle masana’antar, sun ji wa ma’aikata da dama rauni.

Kamfanin ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar.




Lamarin ya faru ne bayan da Gwamnatin Kogi ta bayar da umarni a ƙarƙashin Majalisar Dokokin Jihar Kogi cewa a gaggauta kulle masana’antar, har sai an gabatar da shaidar Dangote ya mallaki masana’antar a bisa tsarin da doka ta tanadar.




Bayyana umarnin ke da wuya matasa da ‘yan bijilante su ka garzaya masana’antar, inda su ka riƙa tilasta ma’aikata cewa lallai sai sun kulle masana’antar.

Kamfanin ya ce zai ci gaba da gudanar da aikin sa kamar yadda doka ta tanadar.




PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Majalisar Kogi ta bada umarnin kulle Kamfanin Simintin Ɗangote.


Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta bada umarnin a kulle Masana’antar Dangote Cement, bisa dalilin wasu zarge-zarge da ƙorafe-ƙorafe da ake yi.


A ranar Laraba ce Majalisar Dokokin ta bayar da umarnin, biyo bayan wasiƙar ƙorafin da mazauna Obajana, garin da kamfanin ya ke, su ka rubuta wasiƙar ƙorafi.





Majalisa ta kira Ɗangote, wanda shi ne na mafi karfin arziki a Afrika, domin ya je ya bayar da ba’asi, amma ya nemi a bayar da isasshen lokaci.


PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Kakakin Ɗangote Cement PLC, Anthony Chiejina, amma bai maida amsar saƙon tes da wakilin mu ya yi masa ba.





Mazauna yankin dai sun rubuta wasiƙar ƙorafin cewa ana ɓata masu muhalli, kuma ba a inganta rayuwar al’ummar yankin, kamar yadda doka ta wajabta wa masana’antar, kasancewa a yankin ne ta ke samun biliyoyin kuɗaɗe a duk shekara.





Ƙorafin da mazauna yankin su ka kai ya tayar da bincike ƙwaƙwaf ɗin da Majalisar Kogi ta ce ta gano cewa Ɗangote Cement ya sayi kamfanin daga Jihar Kogi tun cikin 2002, ba tare da ƙwararan takardun cinikayya ba.




Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwa ne ya sanar da manema labarai haka.


Dalili kenan Majalisa ta bada umarni a kulle masana’antar, har sai an gabatar mata da takardun ciniki.




Dangote Cement ya sayi kamfanin simintin daga hannun Jihar Kogi cikin 2002, a lokacin da ake kiran sa da suna Obajana Cement Company.


Ɗangote Cement a yanzu shi ne masana’anta mafi tsada ta biyu a Najeriya.



Cikin 2022 tsakanin Janairu zuwa Yuni kamfanin ya yi cinikin siminti na naira biliyan 808, wanda a ciki naira biliyan 172.1 duk riba ce ta watanni shida.

Comments