Main menu

Pages

AMFANIN CIYAWAR GOGA MASU HUDU GA RAYUWAR DAN ADAM.
Amfanin Goga masu guda hudu ga rayuwar Dan Adam

Ciyawar Goga masu nada matukar amfani a rayuwar Dan Adam, ana samun ta a duk wani guri da yake iya fitar da ciyawa a doron kasa. 

Ga kadan daga amfanin ta:-


1. Dan magance matsalar fata ana samun ciyawar Goga masu a busar a dake ta zama gari sai a debi cikin babban cokali 1 a kwaba da man shanu ko alayyadi ko zaitun ko habba ana shafawa a duk inda fata keda matsalar makero ko kuraje da sauransu. A kula da awo da adadi idan tayi yawa a hadin tana saka sabar fata kamar sabar maciji. 

2. Ana amfani da Goga masu dan magance matsalar sanyin mara na maza da mata komai karfin shi InshaAllah. Za a samu busasshen garin ciyawar Goga masu babban cokali 5 sai garin sassaken marke babban cokali 10 a hade ana shan karamin cokali 1 a shayi me zafi safe da dare sati daya. 

3. Ga maza masu raunin gaba sai ku hada ciyawar Goga masu da duk wani abu da kuka san ana kira kayan yaji na shayi ku dake kuna shan karamin cokali 1 a shayi me zafi safe da dare sati 2. 
4. Dan neman kasuwa da ciniki kar kuyi shirka kawai ku samu ciyawar Goga masu da gyada me goyo daidai gwargwado ayi dakan turare (kar yayi laushi sosai) sai a kwaba da turaren Binta Sudan da wani turare dan company me suna six flowers ana turare a wajen kasuwanci. InshaAllah za aga canji. 


Wannan hadin kowanne an gwada an dace sai kuyi kokarin gwadawa kuma. 

Sharadi

Kar ku manta da awo da adadi musamman wajen hadin sha da shafawa dan tana da zafi.

Comments