Main menu

Pages

MATAKAI GUDA 4 DA ZA ABI DON KAUCEWA CUTUTTUKAN IDO

 Matakai guda 4 da za a bi don Kaucewa cututtuan Ido.

Hukumar lafiya ta duniya ta ware wannan rana ta 13 ga watan Oktoba a duk shekara domin nuna muhimmancin kula da lafiyar ido da kuma fadakarwa kan halin da mutane suke ciki game da lafiyar idanu a duniya domin kyautata lafiyar idon.


Taken wannan rana a wannan shekara ta 2022, shi ne ‘’Love Your Eye’’ wato Mu Kaunaci Idonmu.


 


A tattaunawar da ta yi da BBC kwararriyar likitar ido a asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, da ke Najeriya, Dr Fatima Kyari, wadda kuma tana daga cikin shugabannin kungiyar yaki da makanta da cutukan ido ta duniya, ta ce taken ranar da ya kasance "Mu Kaunaci Idonmu" na nufin sai mutum ya kaunaci idonsa ne sannan zai san muhimmancin kare shi.
Likitar ta ce a bisa wannan rana ne kungiyar ta duniya ke so ta fadakar da mutane cewa akwai matsalolin na ido da ke damun al’ummar duniya wadanda ya kamata a tashi tsaye domin maganinsu saboda illarsu ga rayuwar dan-Adam, inda za su iya kai shi ga rasa gani gaba-daya idan ba a dauki mataki ba tun daga farkon-fari.
Dr Fatima ta ce a yanzu alkaluma sun nuna cewa a fadin duniya akwai mutum kusan miliyan dubu daya da ke fama da cutukan ido, wadanda ba su da yadda za su yi, wajen neman magani.Saboda ko dai ba su da kudi ko kuma ba su da inda za su je a yi musu magani, wanda wannan ba karamar matsala ba ce in ji kwararriyar likitar. 

Cutukan da ke shafar ido

Ta ce fitattun cutukan da suka fi damun jama’a na ido su ne cutar yana wadda ake kira da Ingilishi ''cataract''.


Wannan cuta takan sa mutum ya rika ganin hazo-hazo idan kuma ba a dauki matakin neman magani ba za ta iya sa mutum ya rasa ganinsa ma baki-daya.


Likitar ta yi bayani da cewa cuta ce da take samun yawanci mutanen da suka girma daga shekara 40 zuwa sama, ko da yake ta ce hatta jariri ana iya samunsa da ita, amma dai galibi ta fi samuwa ga manya.


Alkaluma sun nuna cewa a Najeriya akwai mutum sama da dubu dari daya da ke kamuwa da wannan cuta.


Ita dai cutar ana maganinta ta hanyar yi wa mutum aiki, inda kwararrun likitocin ido ke sauya abin da ke zama kamar giliashin da ke cikin idonsa da wani na likita wanda za a sanya masa a cikin ido ganinsa ya dawo kamar na da.
Sai kuma cutar da ke shafar jijiya da ruwan cikin kwayar ido wadda da Ingilishi ake kira "Glaucoma".


Wannan cuta tana shafar jijiyar ido wadda kwatankwacinta ita ce wutar lantarki da ke sa kwan lantarki haske.


To ita wannan cuta wadda take kama ido a hankali a hankali, ita ma galibi saboda shekaru, tana farawa da ido daya sannan kuma ta kama daya, idan har ba a dauki mataki da wuri ba har ta lalata ido ya kasance mutum ya daina gani to ba wani abu da za a iya yi a gyarawa mutum ido.
Ana iya yi wa mutum aiki a asibiti a rage illar cutar.

Sai kuma larurar kasa ganin abin da ke kusa wadda ita ma yawanci tana shafar idanuwan mutanen da suka zarta shekara 40.


Dr Fatima ta ce ita wannan larura wadda za a ga mutum ba ya iya karatu ko kallon waya sai y aja littafi ko wayar da yake dubawa nesa, matsala ce wadda take samun mutum saboda yawan shekaru, amma ba cuta ba ce.


Likitar ta ce hanyar da ake samun sauki da wannan ita ce ta yadda mutum zai je asibiti a duba idonsa a tabbatar ba shi da wasu cutukan, sai a auna shi a yi masa tabarau, wanda zai rika amfani da shi.


Kwararriyar ta kuma ce akwai cutuka da kan shafi idanu wadanda suke da nasaba da wasu larurorin na lafiya kamar cutar sukari.
Matakan kauce wa kamuwa da cutuka

Kwararriyar likitar idanu, Dr Fatima Kyari ta bayyana wasu daga cikin muhimman matakan da ta ce ya kamata mutane su rika dauka domin kaucewa kamuwa da cutukan ido.


Gwajin idanu lafiyar idanu- da farko ta ce ya kamata tun mutum yana jariri ya kamata a ce daga haihuwarsa an duba idanuwansa an tabbatar ba shi da wata larura.


Sannan a matakin girma na mutum tun daga fara girman mutum kafin ya fara zuwa makaranta da lokacin da aka fara kai shi makaranta ya kamata a rika yi masa gwajin idanu.


Haka kuma idan mutum ya kai munzalin aiki ya kamata a ce kusan a duk shekara biyar yana zuwa ana duba lafiyar idanunsa.


Likitar ta ce amma idan mutum ya kai shekara 40 to ya kamata yadda yake zuwa ana duba lafiyar jikinsa daga lokaci zuwa lokaci ya kamata a duk bayan shekara biyu a duba lafiyar idonsa.


Saboda a cewar likitar cutukan ido fi kama mutum a lokacin da ya kai shekara 40, saboda haka yana da kyau a ce duk wata matsala a jikin mutum an gano ta da wuri domin daukar mataki.


Wasu daga cikin hanyoyin da mutum zai iya kauce wa kamuwa da cutukan ido sun hada da;


-Cin abinci mai kyau, wato mai gina jiki


-Kauce wa yin amfani da magani ba tare da zuwa asibiti wajen kwararru ba


-Yin gwaji akai-akai kamar yadda muka yi bayani a baya.


-Kada mutum ya je kasuwa ya sayi tabarau na likita ya rika amfani da shi ba tare da ya je asibiti an duba shi an ba shi ba.
Yawan masu larurar idanu a Najeriya

Dr Fatima Kyari ta ce a wani bincike da suka yi a baya sun gano cewa a Najeriya  a duk mutum 25 mutum daya na ta cutar makanta.


Sannan kuma idan ana bayani ne na masu sauran cutuka na ido a duk mutum biyar akwai mutum daya da ke da wata larura ta ido.

Comments