Main menu

Pages

WASU DAGA CIKIN DABI'U NA MATA DA KAN JANYO MUTUWAR AURE

 Manyan Dabi’u 11 daga cikin halayen Mata da Ke Kashe Musu Aure:


Wasu daga cikin dabi’un dake lalata Aure ta bangaren Mata sune kamar haka. Mata suna da matsaloli da yawa wanda yake kawo masu lalacewaar aurensu, daga cikin dabi’un dai akwai:


 


- Kwadayi: Da yawa daga cikin mata su kan auri mutum don kwadayin wani abu da ke hannusa, wannan abun shi ne dalilin da ya sa suka yi aure. Bayan an yi aure sun je gidan mijin, za su tsaya su tabbatar da cewa wannan abun da suke so suna samun shi. Idan kuma ya zama ba su samu ba, to za su ta da hankali a kan cewa sai an sake su, wasu kuwa ko da sun samu to duk sanda aka ce wannan abun babu shi ko kuma ya kare to haka suma zaman su da kai ya kare domin abin da ya kawo su ya kare.


 


- Rashin Biyayya: Mata da yawa ba su da biyayya wanda shi kuma namiji yake bukata, sakamakon haka dole ne aure ya rabu saboda rashin zaman lafiya.


 


– Rashin Iya Kwalliya: Rashin iya kwalliya da kuma ado yana kawo rabuwar aure, saboda shi namiji yana son ya ga matarsa cikin kwalliya a kowanni lokaci. Za ka iya samu cewa miji ya kawo duk abin da ake bukata na kwalliya, amma ita kuma matar ba ta yi, to sai ka ga ya fi bukatar zama a waje fiye da cikin gidansa domin sai matarsa ta daina birge shi, daga nan sai yawan fada, sai kuma rabuwa wanda wannan laifin mata ne.


 


– Rashin Iya Girki: Da yawa daga cikin mata ba a koya masu girki a gidajensu wanda sai sun yi aure sannan abun ya zamar masu matsala. Rashin iya girki babbar matsala ce a zaman aure wanda za ka samu cewa duk abin da mace ta dafa babu dadi ko kuma ba a iya ci, shi kuma mai gidan yana kawo duk abin da ake bukata wajen girki amma babu biyan bukata wajen girki wanda daga karshe idan ya gaji sai ka ga ya sake ta wanda wannan matsalar mace ce.


 


– Rashin iya Magana: Wasu matan ba su san yanda za su yi magana da mijinsu ba, sai ka samu cewa ga matar da matukar kyau amma mijin baya gani saboda rashin iya magana, sai ya je waje ya biye wa wanda ba ta kai matarsa komai ba, amma ta iya magana, sai ta dauki hankalinsa wanda daga karshe zai ji ya gaji da ita wannan matar tashi kuma sai ya sake ta ya kawo wata.


 


- Kazanta: Tsafta tana daga cikin abin da zai sa mijinki ya soki, kamar tsaftar mahalli da kuma yara. Namiji yana son ya ga ko da yaushe gidansa da kuma ya ransa da tsafta, amma wannan ya yi wahala a matan Hausa, wanda rashin tsafta zai sa ya gaji da ita saboda kazanta.


 


- Rashin Godiya: Wasu matan ba su da godiyar a kan irin kokarin da mijinsu yake masu, kullum yana bakin kokarinsa amma ba sa gani. Wannan kuma yana kawo matsala daga karshe ka ga an rabu saboda ya gaji.


 


– Rashin Kula Da Dukiyar Miji: Dukiyar miji tana da matukar mahimmanci komin kankantarta, amma da yawa daga cikin mata ba sa gani, sai subar dukiyar mijinsu ta lalace suna gani wanda shi kuma mijin bayan jin dadin haka, idan ya yi iya kokarinshi ba ta daina ba karshe sai ya sake ta.


 


– Gasa: Wasu matan suna da gasar cewa duk abin da aka yi wa wata mace suma sai an yi masu ba tare da kulawa da cewa mazajensu ba karfinsu daya ba. Za ta matsa wa mijinta sai ya yi mata duk irin abin da ta gani a wajen wata macen wanda idan ya gaji ko kuma ba shi da hali, to sai dai su rabu da ita.


 


– Daukar Shawarwarin Banza: Wata macen ba ta da matsala da mijinta amma tana daukar shawarar banza daga ‘yan’uwa da abokai. Sukan ba ta shawarar banza a kan abin da za ta yi wa mijinta ta cutar da shi ko kuma ta hanyar sanya shi abin da baya iyawa wanda idan dai bai yi su ba, to sai dai ya sake ta.


 


– Wulakanci: Mata da yawa sukan so su ringa wulakanta mutanen da suka shafi bangaren mijinsu, kamar iyayensa da yan’uwansa da kuma abokan arzikinsa, domin damar da ta samu na zama matar dansu, dan’uwansu ko abokinsu wanda wasu mazan ba sa yarda da wannan to idan har macen ba ta daina ba to sai saki ya shiga.

Comments