Main menu

Pages

TOFA!!! NIGERIA TA SHIGAR DA COMPANY FACEBOOK KARA A KOTU

 



Tofa! Gwamnatin Nigeria ta gurfanar da Company Facebook a gaban Kotu.

Gwamnatin Najeriya ta shigar da kamfanin Meta, wanda ya mallaki shafukan sada zumunta da muhawara na Facebook da Instagram da kuma WhatsApp a kotu, saboda yin talla a kasar ba tare da bin ka’ida ba.




A karar hukumar kula da tallace-tallace a Najeriya (ARCON) na neman kamfanin na Meta da kamfanin AT3 Resources Limited da ke wakiltarsa a Najeriya su biya ta kusan Dala miliyan 70 kwatankwacin Naira biliyan 30 saboda tallata abubuwa ga ‘yan Najeriya ta shafukan na intanet ba tare da hukuma ta tantance tallace-tallacen ba.





Hukumar tana neman babbar kotun tarayya a Abuja ta zartar cewa tallata wani abu a shafukan intanet na kamfanin na Meta ga ‘yan Najeriya ba tare da hukuma ta tantance ko amince da wannan talla ba abu ne da ya saba doka.





Baya ga zartar da cewa yin tallar ba tare da amincewar hukuma ba, abu ne da ya saba ka’ida, matakin ya kuma sa gwamnati ta yi asarar wasu kudade da ya kamata ta samu ta tallace-tallacen.




Idan har shari’ar ta samu karbuwa har ma gwamnatin ta yi nasara to hakan zai sa Najeriyar ta cimma burinta na kokarin sanya ido tare iko a kan duk wani abu da ke wakana a shafukan intanet a kasar.




Sau da dama gwamnatin Najeriyar na kokarin ganin ta yi iko yadda take so a kan yadda ake amfani da shafukan sada zumunta da muhawara na intanet a kasar domin taka burki ga wasu abubuwa musamman na sukar gwamnati.





Sai dai dangane da wannan kara, gwamanatin ta jadda cewa ba wai tana son takaita ayyukan shafukan sada zumunta da muhawara ba ne a Najeriya, illa dai tana son a bi dokokinta na talla a intanet.




Kamar yadda a watan Yuni ta fitar da daftarin wasu dokoki na yadda kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara za su rika gudanar da ayyukansu a kasar.




A kwanan nan hukumar da ke sanya ido a kan tallace-tallace a Najeriya ta hana amfani da muryar ‘yan kasashen waje ko masu tallata kaya ‘yan waje a Najeriya inda dokar za ta fara aiki daga wannan wata.

Comments