Main menu

Pages

HULUNAN HANA SATAR AMSA DA A KA KIRKIRO DON SAKAWA A EXAMS HALL

 
Hulunan da aka kirkiro domin Hana leken amsar Wani.

Hotunan ɗalibai sanye da wasu hulunan da aka ce na hana satar amsa ne suna yawo a shafukan sada zumunta a Philippines, wani abu da ya janyo cece-ku-ce.
An buƙaci ɗaliban kwalejin Legazpi su sanya abubuwa a kawunansu waɗanda za su hana su leƙen amsoshin waɗanda ke kusa da su.
Da yawa daga cikin ɗaliban sun haɗa hulunan ne ta hanyar amfani da kwalaye ko takardun da aka gama amfani da su.
Malamarsu ta shaida wa BBC cewar ta yi ƙoƙarin nemo dubarar tabbatar da gaskiya wurin jarabawa a tsakanin ɗalibanta

Farfesa Mandane-Ortiz ta ce da farko ta buƙaci ɗaliban ne su haɗa hulunan ta yin amfani da takardu.

Ta yi wannan tunanin ne bayan samun labarin wata dubarar makamanciyar haka da aka yi amfani da ita a Thailand, a shekarun baya.

A 2013 hoton wasu ɗalibai da ke rubuta jarrabawa sanye da kariya a gefen kunnuwansu, waɗanda aka haɗa da takardu, a Bangkok ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.

Farfesar ta ce ɗaliban sun ɗauki wannan salo, inda wani a lokaci suke amfani da duk wani abu da ke kusa da su domin haɗa hular cikin ƙanƙanin lokaci.
Wasu kuma sun yi amfani da malfa, ko hular-kwano ko kuma takunkumin fuska domin yin wannan shinge.

Hotunan ɗaliban, sanye da hulunan, waɗanda farfesar ta wallafa a facebook sun janyo hankalin mutane cikin kwanaki kaɗan, kuma suka janyo hankalin gidajejn yaɗa labaru.

Kuma rahotanni sun ce hotunan sun ƙara wa jami'o'i ƙwarin-gwiwa wajen buƙatar ɗalibansu su yi amfanin da irin waɗannan huluna na hana satar amsa.

Farfesa Mandane-Ortiz ta ce ɗaliban nata sun ƙara ƙoƙari a jarrabawar wannan shekarar, kasancewar tsananin da aka ƙara wurin hana satar amsa lokacin jarrabawa ya sanya ɗaliban sun ƙara himma wurin karatu.
Ta ce da yawan su sun kammala jarrabawar da wuri, kuma babu wanda aka kama da laifin satar amsa.

Comments