Main menu

Pages

YADDA ZAKI KULA DA TSAYUWAR BREAST DINKI LOKACIN SHAYARWA KAR YA ZUBE
Yanda Zaki kula da tsayuwar Breast dinki lokacin Shayarwa.

Nonon mace dayafi kowanne kyau shine ake ƙira (Fundamental straight ) yana jure wahala bayan shayarwa da yawa yana kasancewa a tsaye da taurinsa 

Amma duka haka idan ya haɗu da rashin kula lokacin shayarwa zai iya lalacewa, Domin kula da gyaruwar nononki daga haihuwarki ta fari ki tabbatar kina taka tsantsan yanda za ki gama shayarwa kiyi gyaran nononki ya dawo kamar kina budurwa, wannan shine martaba ta Mace abunda zai ƙara miki daraja a wajen miji,Abu na farko shine ba'a manna bakin yaro akan nipples yanda ba zai sha iska ba haka zalika ba a shayar da yaro nono yana zuba ki kiyaye da wannan,Ba ayin bacci ana shayar da yaro, gaba ɗaya ma ba aso ana shayar da yaro a kwance yanda za ki kwanta akan ɗaya nono kuma kina bashi ɗaya, sannan Yara da suke daɗewa suna sha ana canja musu nono kada ya zama tsawon lokaci yana Shan ɗaya domin haka nasa nono ɗaya yafi ɗaya, kuma nipples ɗin ba zai sha iskaba,Ba ayin jima'i ana shayar da yaro nono sannan ba a kwantar da yaro abashi nono ta sama wato kiyi rubda ciki a kansa,Ba a barin yaro yasha nonon wata daban sannan ya dawo Shan na mahaifiyarsa, Hakan yana banbanta tsosan Wanda Hakan zai kawo yamushewar nipples, Wanda sanadiyar haka nono ya kasa gyaruwa, Hakan tasa wasu na ganin idan mace na shayarwa to kada ta bari mijinta yana tsotsa yanda yaron yake, ya samu wani salo na daban Wanda tsotsansa bazai rinka zubo da ruwan nono ba.Sannan kuma Hakan baya hana kiyi abinda ake cewa (multiple peeding) wato idan kina shayarda yaronki ki hada da wani yaron, abunda dai ba aso yasha nonon wata kuma kema yana shan naki,Ba a barin farin nono dake zuwa ya gushe kafin a fara shan maganin yaye, da zaran lokacin yaye ya kusa idan kika fuskanci ruwan nonon ya fara komawa kamar ruwan famfo to kiyi maza ki fara domin idan wannan farin ya gushe kafin nono ya dawo ana shan wahala.

Comments