Main menu

Pages

YANDA AKE MAGANCE CUTAR KIDNEY STONES KO KIDNEY INFECTION
Yanda Za a Magance Cutar Koda Kidney Stones ko Kidney Infection


Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.


Da farko idan aka ce kidney ana nufin koda wasu kananan abubuwa ne a jikin ka,daga kasan bayan ka masu kama da wake guda biyu,gefen dama da gefen hagu.


Suna tace abubuwa mara sa kyau daga jinin ka zu fitar dashi ta hanyar fitsarin ka,sannan suna daidaita ruwa da wasu sinadarai na jikin ka kamar acid gishiri da sauran su da suke cikin jinin ka.


Kidney infection mafi yawan lokaci yana samuwa ne daga kwayar cuta mai suna Escherichia coli (E. coli)


Kuma ana samun wanna cuta a cikin hanjin mutum,wacce take samun isa ga kodar ka ta hanar fitar fitsarin ka wato (urethra).


Wannan infection yana tafiya daga hanyar fitar fitsari zuwa wajen tara fitsari (bladder)har zuwa kodar ka.


Sannan ana samun wannan infection daga wani waje a cikin jikin ka,kama daga gwiwar ka subi har zuwan hanyar jinin ka.

Ko kuma wadan da aka yiwa aikin mafitsara ko aiki a koda.


Abubuwa da suke toshe hanyar fitsari, kamar kidney stones wato tsakowar koda,kurji ko kumburi a Furustuta (prostate)


Sannan mata sunfi saurin daukar wannan cuta fiye da maza,saboda hanyar fitsarin su tafi gajarta akan ta maza.


Mace mai ciki ma tana cikin barazana da hadarin kamuwa da wannan cuta.


Wadan da suke fama da raunin garkuwar jiki,hadi da masu ciwon suga,hiv da sauran su.


Alamomin Kamuwa da Wannan Cuta.

1. Ciwon baya, ko ciwon gefe daya na baya daga sama.

2. Yawan tashin zuciya

3. Yawan jin amai 

4. Kuna ko jin zafi wajen fitsari.

5. Fitsari me kala.

6. Zazzabi

7. Jin sanyi.


Hanyoyin Kaucewa wannan Cuta.

1. Yawan shan Ruwa

2. Dena rike fitsari na tsawon lokaci.

3. Yin fitsari bayan jimai.

4. Kayi kokari ka rika gama fitsari baki daya.


Maganin ga wadanda wannan Cuta ta kama.

Za a Nemo;

1. Ganyen mankwaro guda 5

2. Lemon tsami guda daya

Za a yanka lemon tsamin kanana,sannan a jajjaga ganyen a hada da ruwa Liter daya a dafa sha safe da yamma.

Comments