Main menu

Pages

YANDA AKE HADA FRUIT SALAD MAI MADARA.

 Yadda ake hada Fruit Salad Mai Madara


Abubuwan hadawa 

Abarba

Kankana

Gwanda

Ayaba

Tuffa

Lemon

Madara

Yadda ake hadawa


Da farko za ki gyara kayan marmarinki sai ki dauko kwano mai kyau da wuka sai ki yanka kanana kamar girmar maggi (cube)


Idan kinzo ayaba za ki cire bakin tsakiyan sai ki yanka haka za ki yima tuffa sai ki matsa lemon juice rabin


Idan kin gama sai ki saka kankara ko ki sa a firinji idan ya yi sanyi sai ki sa madara ki juya sai ki zubawa maigida da yara

Karin bayani


Madarar za ki iya sa ta ruwa ko ta gari sannan kuma ba sai kin sa sugaba.

Comments