Main menu

Pages

TOFA! A KARSHE DAI BUHARI YA MAKA KUNGIYAR ASUU A KOTU

 Shugaba Buhari ya Maka kungiyar ASUU a kotu, saboda abin yakici yaki cinyewa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gurfanar da kungiyar malaman jami'o'i ta kasar the Academic Staff Union of Universities (ASUU) a gaban kotun ma'aikata game da yajin aikin da suka kwashe wata bakwai suna yi.


A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar kwadago ta kasar, Olajide Oshundun, ya fitar ranar Lahadi, ya ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa tsakaninta da kungiyar malaman jami'o'in ta ci tura.


Gwamnati tana son kotun ma'aikatan ta bai wa mambobin ASUU umarnin su koma bakin aiki, a yayin da ake ci gaba da shari'a a kan batun.


Ana sa rai kotun za ta soma sauraren karar a yau Litinin.


Kazalika gwamnatin tarayya tana son kotun ta bayyana halasci ko haramcin yajin aikin na ASUU.


Haka kuma gwamnatin tana so kotu ta yi fashin-baki kan dokar kwadago mai sakin-layi 18 LFN 2004, musamman hukuncin yajin aiki a yayin da tattaunawa ke ci gaba tsakanin ministan kwadago da malaman jami'o'i.


A makon jiya Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa sun yi iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen yajin aikin na ASUU.


ASUU ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar.

Comments