Main menu

Pages

KOGIN TIGA NA KANO YA HADDASA AMBALIYA A WASU YANKUNAN

 



Yanda Kogin Tiga na jihar Kano ya haddasa ambaliya a wasu yankunan na jihar

Daruruwan mutanen da ke kananan hukumomin Warawa da Bunkure da Wudil da kuma Rano a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na cikin zulumi saboda ambaliyar ruwan da ake fuskanta sakamakon bude wasu hanyoyin madatsun ruwa na dam din Tiga.


 Hukumar da ke kula da kogin Hadeja Jama’are ce ta bude madatsun ruwan saboda taruwar da ruwan ya yi.


Ta ce bude madatsun ruwan za ta hana kogin yin ambaliya lamarin da ka iya haddasa rasa rayukan jama'a .



 Tuni mazauna kauyukan da ke kusa da madatsun ruwan suka bar muhallansu saboda yadda ruwan ya kewaye garuruwansu.


 Kauyen Gishirin Wuya na daya daga cikin kayukan da ke karamar hukumar Warawa da ruwan ya mamaye, kuma tuni mazauna kauyen suka bar gidajensu don tsira da rayukansu.


 An kiyasta cewa akwai mutane dubu biyu da ke zaune a kauyen.


Mazauna kauyukan sun ce sun fada cikin zulumi


Kogin Tiga ya yi matukar tumbatsa yana shirin fashewa



Wasu daga cikin mazauna kauyen sun shaida wa BBC cewa ambaliyar ruwan ta yi musu matukar barna, saboda ruwa ya shafe gidaje da gonakinsu.


 Sun ce sun fice daga gidajensu saboda ba su da inda za su zauna.


Ana daukarsu - maza, mata da kananan yara - a kwale-kwale don tsallakar da su zuwa garuruwan da ke makwabtaka da su.


 Mutanen sun kuma yi korafin cewa tun bayan da masifar ambaliyar ta afka musu babu wanda ya kai musu dauki.


 A garin Rurum da ke karamar hukumar Rano kuwa, manoma ne suka koka kan yadda ruwan ya shafe musu gonaki.


 Daya daga cikin manoman ya shaida wa BBC cewa ruwan ya lalata shukar da ya yi ta masara da waken suya.


Ya ce bayan da ya yi shukar ya sa ran zai samu amfani gona mai yawa musamman waken suya to amma yanzu ya rasa komai.



Su kuwa al’ummar kauyen Malam da ke garin Wudil sun shaida wa BBC cewa amfanin gonar da suka shafi shuka a bana ya lalace sakamakon ambaliyar ruwan na Tiga dam.


 Tuni dai hukumomi hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kano SEMA ta ce tana iya bakin kokarinta wajen taimaka wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.


 Kazalika kuma mahukunta a Kanon sun gargadi mazauna yankunan da ke kan hanyoyin da wannan ruwa na Tiga da ya hade da Kogin Hadeja Jama’are ya bi da su bar garuruwansu don kaucewa ambaliyar ruwan.


 A bana dai an samu ambaliyar ruwa da dama a jihohin Najeriya ciki kuwa har da Kano da Jigawa da Bauchi da sauransu.


 Kuma ambaliyar ta haddasa asarar rayuka da dukiya da kuma amfanin gona baya ga rusa gidaje. 


Ana alakanta afkuwar ambaliyar ruwa da rashin magudanan ruwa. To Allah Ya kyauta Ya sa muga karshen wannan Damunar Lafiya.



Comments