Main menu

Pages

SHIRYE SHIRYEN BIKIN SHAHARREN MAWAKI DAN MUSA DA SALMA AMARYAR SA

 



Shirye shiryen Bikin Mawaki Dan Musa ya kankama, shi da Amaryarsa Salma.

An Fara Shagalin Bikin Mawaki Dan Musa Da Amaryarsa Salma. Zuwa Yanzun Shirye Shirye Sunyi Nisa Wajen Tsara Yanda Shagalin Bikin Nasu zai kasance.



Za ayi Bikin Ne Ranar Asabar 17, Ga Watan September Na Shekarar 2022. Za a Daura Auren Ne A Hausawa Masallacin Murtala Ciki Garin Kano, Da Misalin Karfe Goma Na Safe.



Mawakin Dai Yana Daya Daga Cikin Wanda Tauraruwarsu Ke Haskawa A Bangaren Wakokin Hausa, Domin Kuwa Ba Jimawa Su Saki Wata Wakarsu Tare Da Mawaki Ado Gwanja, Waka Mai Suna Kantun Ghana.



Mawakin Ya Shahara Wajen Raira Wakokin Siyasa Inda Zamu Iya Cewa Sune Suka Daga Darajarsa A Bangaren Wakoki.


Muna Fatan Allah Yasa Ayi Shagalin Bikin Lafiya, Allah Kuma Ya Basu Zaman Lfy.

Ga video pre - wedding dinsu ku kalla 



Comments