Main menu

Pages

TATTAUNAWA DA KAWU DAN SARKI MAI WAKAR INGALLO

 Fira da kawu Dan Sarki Mai wakar Ingallo

A yau munzo muku da wata tattaunawa da jaridar Rariya tayi da shahararren mawakin mai wakar ingalo Kawu dan sarki wanda yake bayyanawa mutane irin yadda ya samu daukaka a fagen waka.


Shahararren Mawaƙin Soyayyar Kuma Wanda Tauraruwarsa Ke Haskawa, Muhammad Khalid, Wanda Aka Fi Sani Da Kawu Ɗan Sarki Ya Ce Bai Taɓa Zauna Wa Ya Rubuta Waƙa Kafin Ya RerataMuhammad Khalid Ya Bayyana Haka Ne A Wata Tattaunawa Ta Musamman Da Rariya A Katsina A Satin Da Ya Gabata


Fasihin Mawaƙin Wanda Ɗan Asalin Jihar Bauchi Kuma Yanzu Sun Dawo Kano, An Haife Shi Shekara 28 Da Suka Gabata. Ya Yi Karamar Sakandire Da Babbar A Bauchi Da Kano. Sana’arsa Ta Farko Ita Ce Aikin Kafinta, Amma Da Ya Lura Allah Ya Bashi Baiwar Waƙa Ya Koma Studio.Kawu Ɗan Sarki Ya Kara Da Cewa Babu Inda Na Yi Amfani Da Kalmar Batsa A Cikin Wakokina, Amma Ina Zurfafa Kalamaina Su Yi Nauyi Ta Yadda Waƙata Za Ta Yi Kwari. Babban Burina In Bar Baya Mai Kyau Ba, Saboda Nasan Da Cewa Lokaci Ne Kuma Ina Son Na Raini Masu Tasowa.Muhammad Khalid Ya Cigaba Da Cewa Kalubale Da Nake Fuskanta Shi Ne Ko Ina Ana Sauraren Wakokina, Wasu Na Tunanin Girman Jiki Ne Ya Kawo Haka Ko Kuma Kuɗi Ne Da Ni, Kamar Yadda Muryata Ke Yawo Suke Gani Kuɗi Ne Tattare Da Ni, Alhalin Ba Haka Bane. Wasu Za Su Kawo Maka Matsalarsu Ta Dubbani, Wadda Nima Da Matsalar Za Ta Same Ni Sai Na Nemi Dauki.Daga Karshe Ina Miƙa Dumbin Gaisuwa Ga Masoyana Duk Inda Suke A Faɗin Duniya. Amma Ina Fuskantar Kalubale A Wajen Kiran Da Suke Man A Waya, Su Dunga Yi Man Uzuri Saboda A Rana Ina Karɓar Waya Sama Da Dubu Biyu. Idan Na Ki Daukar Waya Sai Su Dauka Girman Kai Ne, To Ba Haka Bane Su Yi Man Uzuri.

Comments