Main menu

Pages

YANDA WATA DAMISA TA KWACE TA BAZAMA CIKIN GARI

 Wata Damisa ta kwace ta bazama cikin Gari.

An kwashe sama da kwana 27 ana kokarin farautar wata katuwar damisa da ta tsere daga gandun daji a jihar Karnataka da ke kasar Indiya.A ranar biyar ga watan Agusta ne tserewar damisar ta fara daukar hankali, lokacin da ta farmaki wani lebura tare da ji masa ciwo a arewacin birnin Karnataka mai dimbin jama'a.


Tun daga wannan lokaci ake samun labarin ganinta lokaci zuwa lokaci a yankunan birnin, lamarin da ya jefa al'umar jihar cikin halin firgici.Hukumar kula da gandun dajin jihar ta tura jami'ai kusan 300, kama daga likitocin dabbabi zuwa kwararru wajen sanin halayyar dabbobi, domin farauto damisar da nufin mayar da ita gandun dajin. Amma har yanzu sun kasa kama ta.Lamarin dai na neman rikidewa zuwa siyasa, inda 'yan adawa ke ta kiraye-kiraye ga ministan gandun daji na jihar ya sauka, amma Mista Katti ya ce zai yarda ya ajiye aikinsa matukar hakan zai yi sanadin kama damisar.Game da matsin lambar da ake ci gaba da samu kan farautar damisar, wani babban jami'in gandun dajin jihar, Vijayakumar Gogi, ya shaida wa BBC cewa an tura jami'ai masu dimbin yawa domin samun nasarar aikin.


Damisar dai na daga cikin dabbobin dawa da ke da dabi'ar kunya, to amma a 'yan shekarun nan ana samun yawaitar rahotonnin ganinsu a wasu kauyuka da biranen Indiya, a kokarin da suke yi na neman abinci, a yayin da dazukan da suke ciki ke ci gaba da raguwa.Jihar karnataka - wacce ke da yalwar gandun daji tare namun dawa masu dimbin yawa - ita ce jiha ta biyu mafi yawan damisa a kasar inda take da damisa akalla 1,783, kamar yadda wasu alkaluma da gwamnatin kasar ta fitar suka nuna.


Ana yawan ganin dabbobin a manyan biranen jihar, da suka hada da Bangalore da Mysore.


Anthony S Mariappa, babban jami'in da ke jagorantar farautar, ya ce wannan shi ne karo na farko da aka ga damisa a birnin Belgaum, abin da ya sa dole mutane su firgice a cewarsa.Yaya ake gudanar da farautar?

An girke kusan kyamarori kimanin 20 a sassa daban-daban na yankunan da ake ganin damisar domin daukar hotunanta.


An kuma ajiye kejin karfe guda 10, tare da karnukan farauta da kuma sauran dabbobi masu sansanar warin abu daga nesa, tare da tarkuna masu tarin yawa, domin kama babbar.Me ya sa har yanzu ba a kama damisar ba?

Mista Mariappa ya ce sau biyu ana ganin damisar lokacin farautar, sai dai takan yi layar zana kafin a kai ga kamata.


Ya kara da cewa mamakon ruwan sama da jihar ke fuskanta na kawo wa farautar cikas, inda ruwan ke tafiya da tarkunan da aka kafa a wurare da dama.


"Haka kuma akwai wadatar abincin damisar a cikin dajin, don haka ba ta damuwa da dabbobin da muke sakawa a jikin tarkon," in ji shi.Wacce shawara masana ke bayarwa?

Sanya Gubbi, wani masanin halayyar dabbobi a jihar, ya ce fahimtar halayyar dabbobin zai taimaka matuka wajen rage firgicin da jama'a ke ciki idan irin hakan ta faru.Ya kara da cewa babban abin da ake bukata shi ne wayar wa mutane kai dangane da sanin halayya da dabi'un damisa, wannan zai taimaka matuka wajen sanin yadda za a zauna da dabbar lafiya ba tare da cutar da al'umma ba.

Comments