Main menu

Pages

 Labarina episode 1 season 5 full movie

Labarina shiri ne mai dogon zango wanda kuma ya samu karbuwa sosai a wajen mutane wanda gidan talabijin na arewa24tv ke haskawa a duk bayan sati daya wanda ake sanyawa ranar juma’a da misalin karfe takwas tun daga zango na farko har zuwa zango na hudu.A yau kuma an sake dawowa tafiya dogon hutun da akayi bisa tsayawa aikin wannan shirin tare da maye gurbin wasu jarumai da bazasu sake haskawa a fim din ba duba da kwantaraginsu ya kare.Wanda a yanzu dai babu jarumi Nuhu Abdullahi wanda ake kira da suna Mahmud a cikin wannan shirin yayin da ita kuma Nafisa Abdullahi ake kiranta da Sumayya wanda sun taka rawar gani sosai a cikin wannan shiri.To nesa dai tazo kusa, ga cikakken video nan episode 1 season 5. Sai dai akwai tallar sosai a farkon film din sai kuyi hakuri ku wuceta don shiga tsundum cikin Shirin.
Comments