Main menu

Pages

MU KOMA KITCHEN (YANDA AKE YIN SUNASIR)
Yanda Ake yin sunasir mai kyau da dadi.

Shidai sinasir kaman Masa yake wato waina, anaci da miyar ganye shima. Abubuwan da Zaki bukata sune kamar haka;


Abin da za a nema

☆Shinkafar tuwo

★Gishiri

★Mangyada

★Baking powder

★Yeast


Yanda za a hada;

Zaki tuka tuwon shinkafa kaman gwangwanin madara daya, sai ki nemi shinkafarki ta tuwo dai dai yawan iyalinki, ki jikata ko ta kwana ko awa daya ma zatayi, sai ki wanke ta ki kai nika, kafin ki tafi sai ki dauko tuwon shinkafar ki murjeshi sosai cikin jikakkar shinkafa da zaki kai nika sai ki kaita a markada su tare. Ki zuba yeast dinki 1/2 teaspoon, sai ki rufe ta zuwa awa daya sai ki bude kisa gishiri kadan da dan sugar sai ki rufe ki shirya toyawa amma kwabin sinasir zai fi ruwa kadan ki dauko non-stick frying pan, kisa a wuta ki shafa mashi mangyada, kafin ki fara zakisa baking powder itama, sai ki duba in ya yi zafi sai ki fara idan kika zuba kaman xa ai pancake zai baje a haka sai ki rufe idan yayi a sai a juyashi har a a gama

Ana cin shi da miyar kabewa da alayyahu ko dage dage. Allah yasa mu dace amin.


Comments