Main menu

Pages

INNALILLAHI.. ALLAH YA KARBI RAN YAKUBU KAFI GWAMNA (BANKAURA)

 Allah Ya karbi rayuwar Umar Malumfashi da akafi sani da Yakubu Kafi Gwamna.

A kwanakin baya mun kawo maku labarin cewa Umar Malumfashi Bankaura da akafi sani da Kafi Gwamna a Shirin kwana Casa'in bashi da Lafiya inda Mainshirya mujallar film yaje asibiti domin duba shi har ma dakyar ya gane Jarumin saboda halin jinya da yake ciki.Inda Umar Malumfashi (Yakubu Kafi Gwamna) yace kazo a lokacin da bazan iya doguwar magana da Kai ba, amma ku tayani da addu'a Allah Shi yasan yadda zai da bayinsa.To a daren jiya Allah Ya karbi rayuwar wannan bawan Allah. Muna fatan Allah Ya jikansa Ya gafarta masa. Ga cikakken rahoto daga tashar tsajar gida.

 


Comments