Main menu

Pages

HADEWAR MURJAR TIKTOK DA 442 DA FARA WAKA YA JANYO CECEKUCE.

 Hadewar Murjar TikTok da Mr 442 da yadda ta fara Waka dashi ya janyo cecekuce.

Cikin 'yan kwanakin nan ne aka ga Murja Ibrahim Kunya shaharriyar 'yar TikTok din nan ta hade da su Mr 442. Har tazo tana maganganun cewa an hada ta kwana da Maza a hotel.
To kamar dai wasa sai ga video ita Murja din tana tuka wata babbar mota a cikin Garin Abuja ita da wasu Mata, sai Kuma gata cikin hotel da Abinci kala kala a gabanta.
To karshen tikewa sai gata tana RERA WAKA kamar yadda Safara'u dai ta fara, itama tayi wata Waka tare da sabon ubangidanta na yanzu wato 442.
Hakan yasa mutane sukayo caa a kanta da zagi da aikatawa saboda ko a da ma tana Shan zagin balle yanzu. To ganin itama ta dauko irin hanyar da Safara'u ta biyo, yasa mutane ke ta korafe korafe, don ganin cewa Murja zata iya doke Safara'u a iya shege.
In har ba a yi wasa ba itama sai an ganta a munin halin da ake ganin Safara'u a ciki koma Fi, saboda Murja a fetsare take dama. To a haka hukuma sunaji suna gani suke barin mutum irin 442 yana lalata yaran mutane, Yana koya masu Waka, wakar Kuma ta iya shege.
Amma anyi shiru sai wasu daban Ake zargi. To Muna rokon Allah da ya kawo mana karshen wannan bala'i da ake janyo mana. Allah Ka shirya Shugaban shaidanu 442 Ka dorar dashi hanyar gaskiya dashi da dukkan mukarrabansa, da duk Wani da ke yunkurin bata tarbiyya diyan Musulmi Ameen Ameen.
Da nayi niyyar Sanya maku wakar ku kalla to Amma sai na fasa, saboda rashin amfanin haka, don yada barna Shima barna ne  Allah Ya shiryemu Ya shiryesu gaba dayan su. Alfarmar Annabi Muhammad SAW.

Comments