Main menu

Pages

MAHAIFIYAR UMMITA DA DAN CHINA YA KASHE TAYI CIKAKKEN BAYANI

 Cikakken bayani daga Mahaifiyar Ummulkhair wadda Dan China ya kashe a Kano.


Mahaifiyar Ummulkhairi Buhari wacce aka fi sani da Ummita ta shaidawa majiyar Taskar Labarai cewa tun farko margayiyar ta hadu da Saurayin nata dan China ne a Shoprite lokacin ta je sayen Turare sai kawarta ta hada ta dashi.Ta ce sun shafe kusan shekara Biyu suna tare to da aka zo maganar Aure sai yan uwan Baban Ummita suka ce ba zai yiwu ta aure shi ba donin dai Mahaifin Ummita ya dade da rasuwa don haka dole yan uwan babanta ne zasu iya aurar da ita a bisa musulunci.Mahaifiyar margayiyar wacce ke sharba kuka ta cigaba da cewa Ummita sun rabu da Mista Geng har ta samu miji tayi aure kuma auren soyayya to amma Allah ya kawo karshen zamansu “kodayake ta ce mijin ya rika zargin Ummita na yin “chatting” da tsohon saurayin nata dan China”Bayan mutuwar aurensu sai Ummita ta dawo gida inda Mista Geng ya rika zuwa akai-akai kuma Ummita bata jin dadin yadda yake yawan nace mata saboda haka har ta daina fita su gana tsawon lokaci Dan China yana zuwa amma haka zai gaji yana buga kofa taki fitowa har dai ranar Juma’a (jiya kenan) ana ruwa sai yayi ta buga kofa tsawon lokaci kafin daga bisani Ummita ta roki mahaifiyar ta taje ta kwatar mata yancinta ta gaya masa ba zata fita ba,Taskar Labarai ta ruwaito Ummita ita ce babbar diyar ta amma tana da kanni maza da mata amma kuma a lokacin da mista Geng ya zo babu mazan a gida, don haka bayan ta bude masa kofa kawai sai ya tunkude ta gefe ya afka cikin gidan


Ko kafin ayi aune Dan China ya kutsa har dakin Ummita ya rufe ta duka tare da sossoka mata wuka,Mahaifiyar Ummita ta ce dama yana shiga gidan kuma ya san dakin Ummulkhairi kodayake tace ba da son ran su yake shiga ba kuma tayi yunkurin hada shi da yan sanda amma yan uwan Ummita a lokacin suka ce kada a kai kara wajen yan sanda domin haka zai jawo ma Ummita bacin suna a wajen jama’aSai dai rashin kai kara wajen yan sanda ya jawo a jiya Mista Geng ya aika da Ummita lahira domin kuwa Mahaifiyar Ummita ta ce tayi ta ihu tana kururuwar neman wanda zai kawo masu dauki amma ba kowa domin dare yayi wajajen karfe 9:00pm na dare ne kuma ana ruwan sama babu kowa a waje, dakyar wani mutum ya zo ya haura ta taga (Window) ya kwaci Ummita inda aka garzaya da ita Asibiti amma rai yayi halinsaMahaifiyar margayiyar ta cigaba da cewa an kama Dan Chinan amma ya kubuce ya tsere sai daga bisani aka sake kama shi kuma yanzu haka yana hannun hukuma, tana rokon a bi masu hakkinsuTaskar Labarai ta kalli wasu hotunan auren Ummulkhairi da kuma bidiyon Ummita a lokacinda suke soyayya da dan China inda aka gansu suna shan soyayya lamarin da ya jawo cece-kuce kodayake Mahaifiyar Ummita ta ce sun yi bakin kokarinsu domin su kore shi amma abun ya faskara domin ba zata aure shi ba amma shi ya kasa fahimtar hakanTuni dai akayi Jana’izar margayiyar a gidansu dake Janbulo a jihar Kano kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.Comments