Main menu

Pages

MATAKAN DA AKE BI WAJEN GYARAN JIKIN AMARYA SATI DAYA KAFIN BIKI
Yanda Ake gyaran jikin Amarya sati daya kafin Biki.

Mataki mataki da za abi don gyaran jikin Amarya, ana saura sati daya kafin Biki. Don haka ku biyomu a wannan posting don ganin yadda za ayi.

Domin taushin fata da sheki

- Man zaitun

- Lalle

- Kur-kur

- Madara peak


Zaki hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, zakiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki shiga wanka jiki yana yin kyau yayi sheki


Gyaran jikin Amarya na biyu

- Kur-kur

- Dulka

- Zuma

- Kwai

- Lemun tsami


Ki hade su guri daya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki Idan kuma har dajiki kikeso, sai ki shafa harda jiki

Bayan (1hr) sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge

 


Gyaran jikin Amarya kashi na uku

- Lalle

- Kwaiduwar kwai guda 3 ( yellow )

- Manja cokali 3

- Kur-kur

Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa (1hr) daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka

 


Gyaran Fuska na daya

- Dettol

- Sabulun Ghana

-  Garin zogale

- Farar albasa

Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi.


Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri takuma Kore kurajen fuska.

- Bawon Kankana

A samu bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumulGYARA KAFA:

Baki ba zuwa wajen wanke kafa I'm har kinyi amfani da wannan hadin


🌸¶ man shanu

🌸¶ man kwakwa

🌸 man ridi

🌸 man alayyadi

Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi da daddare zaki hada wadannan mayamayen guri daya ki shafa a kafa in zaki kwanta bacci daddare sai ki daure da Leda da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man riddi.

Comments