Main menu

Pages

MANYAN GWALAGWALAI MASU DARAJA DA ZA A RUFE QUEEN ELIZABETH DA SU.

 



Shirye shiryen binne Queen Elizabeth, An fitar da Zinaren da za a rufe ta dasu.

Kayan ƙarau

Da yawanmu da zarar mun yi tunanin Iyalan gidan sarauta, abin da ke fara zuwa ranmu shi ne gwala-gwalai da Diamond.


Mulkin mallakar masarautar Birtaniya shi ne mafi girma a tarihin ɗan adam, inda ya bai wa iyalan masarautar damar mallakar mafi girma da kyawu na zinare da gwal.


 Daiman mafi girma na duniya shi ne mai darajar karat 530.2 na Star of Africa. Da shi aka yanka aka yi kambun masarautar. Haka ma diamond mafi shahara na Koh-i-Noor da Birtaniya ta samu bayan da ta mamaye Punjab a 1849.


 Da farko Sarauniya Victoria ke amfani da shi kamar ɗan maɓalli. Daga baya aka saka shi a kambun Sarauniya Alexandra kana daga bisani aka saka shi a kambun naɗin sarautar Mahaifiyar Sarauniya a 1937. Baya ga kayan ƙarau na masarautar, Sarauniya Elizabeth na da gwala-gwalai na ƙashin kanta da dama da ma duwatsu masu daraja.


Sai dai an fi ganin Sarauniyar ne yawanci da ɗan kunneta na dutse mai daraja ɗan manne da sarƙarsa - wanda hakan ya zama kamar wani salon adonta na musamman.



Hoton sama da na kasa, saurauniyar England sanye da dutsen diamond sarka da Dan kunne.


Jana'iza

Ana tsammanin Sarauniya Elizabeth ta miƙa kusan dukkan kayan ƙarau ɗinta ga ɗanta, Sarki Charles. Amma wani ƙwararre kan harkar masarauta ya yi hasashen cewa za a binne ta da wasu setin sarƙarta biyu daga cikin abin da ta mallaka. 



Lisa Levinson, shugabar sadarwa ta Cibiyar Zinare, ta ce ta yi amanna setin da za a zaɓa ɗin za su kasance zinare ƙirar yankin Welsh na aurenta ne da kuma ƴan kunne biyu na dutse mai daraja.


To maji Kuma ma gani idan har zasu amfaneta a inda take a halin yanzu.

Comments