Main menu

Pages

KO KUN SAN AMFANIN YALO DA MUHIMMANCINSA GA LAFIYAR MU

 



Amfanin yalo da muhimmancinsa ga lafiyar jikin Dan Adam:


Bincike da dama da masana suka gudanar ya nuna cewa yalo ya samo asali ne daga kasashen India da kuma Afirka, amma kuma yanzu ana noma shi a fadin duniya.


A Najeriya an fi noma yalon ne a yankin arewacin kasar inda akan kuma same shi a kasuwanni daban-daban a fadin kasar.


Za a iya cin danyensa wanda wasu sukan hada da soyayyiyar gyada ko su rika dangwalawa a hadadden garin yaji ko kuma soyayyiyar miya su rika ci.


Daya daga cikin abubuwan ban mamaki game da yalo shi ne yana fitowa a nau'uka daban-daban, wanda ya danganta da yanayi da kuma wurin da ake nomawa.


Yana kuma fitowa a launuka da kuma fasali da girma da kuma dandano daban-daban. Akan samu masu launkan fari, da ruwan goro, da kore, da algashi da dai wasu launuka.


A kudancin jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya akwai kabilar Baburawa da kan yi amfani da gauta wato daya daga cikin nau'in na yalo wajen abinci, su kan rika hadawa da tuwo suna gutsura suna ci.


Malama Adama Hassan wacce 'yar kabilar Babur din ce da ke zaune a garin Biu na jihar Borno inda Baburawan suka fi yawa, ta shaida wa BBC cewa suna matukar muhimmantar da Yalo ko data, ko kuma gauta a matsayin cimaka.


''A ko da yaushe ba za ka taba rasa gidan Baburawa da gauta ko yalo ba, saboda muna hada shi da abinci, musamman tuwo, yana a matsayin miya ne, mu kan rika gutsurar shi mu hada da tuwo muna ci.''



Amfanin yalo ga lafiyar jikin dan adam

Galibin mutane na cin Yalo ne kawai don nishadi ko kashe yunwa ba tare da fahimtar irin dimbin amfanin da yake da shi a jikinsu ba.


A nan za mu duba amfanin yalo da kuma muhimmancin sa a jikinmu. Ba zai yiwu mu kawo duka ba, to amma za mu tsakuro kadan daga cikin amfaninsa:


Kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta Medical News Today da ke Amurka ta wallafa, binciken da masana da dama suka gudanar game da yalon ya nuna cewa yana da matukar amfani ga lafiyar jikin dan adam kamar yadda 'ya'yan itace suke da shi.


Jerin wasu daga cikin amfanin yalon:

1. Rage kiba;

Kamar yadda Mis Megan Ware wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki a Amurka kuma manomiyar kayan lambu ta wallafa a mujallar Medical News Today, yalo na da matukar amfani wajen rage kiba saboda yana kunshe da sinadaran da ke taimakawa kona kitsen jikin mutum wanda kan sa a rage kibar.


Malama Husna Abubakar wacce ke zaune a garin Abuja babban birnin Najeriya ta shaida wa BBC cewa maigidanta wanda ke da kiba sosai ba ya rabuwa da sayen yalo saboda yana da yakinin cewa yana da matukar amfani wajen rage kiba.


''Na ga yana yawan sayen yalo kuma yakan saka ni in yanka masa kanana kamar yadda ake yanka su kankana in kawo masa a ko wane dare ya ci kafin ya kwanta,'' in ji Husna.



2. Kare garkuwar jikin dan adam

Kamar yadda mujallar Healthline ta Birtaniya ta wallafa a wata majalar kiwon lafiya, sinadaran Anthocyanins, da nasunin da kuma flavonoids sinaran kashe kwayoyin cuta ne masu karfi da ke kunshe cikin yalo da kuma kan taimaka wajen bayar da kariya ga garkuwar jikin dan adam tare da kara inganta lafiyar jikin.



Sinadarin Anthocyanins na tainama wa wajen bayar da kariya daga yaduwar kwayoyin halittar da ke haddasa cutar kansa har ma da sauran cututtukan da kwayar cutar bacteria ke haddasawa.



3. Inganta aikin jijiyoyin jini

Yalo yana kunshe da sinadaran vitamin B kamar su thiamin, da niacin, da B6 da kuma pantothenic acid wadanda ke taimakawa wajen amfani da sinadaran fat da na protein; kana suna bayar da gudumawa mai amfani ga hanyoyin jijiyoyin sadarwar kwakwalwa.



Sinadarin vitamin B na taka muhimmiyar rawa wajen inganta kiwon lafiya. Yana taimaka wa wajen inganta aikin kwakwalwa tare da tabbatar da cewa hanyoyin jijiyoyin sadarwar kwakwalwa da na garkuwar jikin dan adam na aiki yadda ya kamata.



4. Karfi da lafiyar kashi

Saboda sinadaran minerals irin su folate, da manganese, da vitamin K, da magnesium, da vitamin da kuma Copper da yalon ke kunshe da shi, yana taimaka wa wajen kara karfi da lafiyar kashi in ji Mujallar Medical News Today ta Amurka.

Cin yalo a ko da yaushe yana da matukar muhimmanci wajen bayar da kariya daga hadarin lalacewar kashi da kuma rashin kwarin kashi.



5. Narkar da abinci a jiki

Kamar yadda bayanai suka nuna daga farko, yalo na da sinadarin da ke taimaka wa sosai wajen narkar da abinci a jikin dan adam (fibre) tare da taimakawa a yanayin yin bayan gida.


Saboda wannan sinadarin da ya kunsa, suna rage yawan kumburin ciki da rashin yin bayan gida sosai ta hanyar inganta narkewar abincin.


Sinadarin na matukar taimakawa a lafiyar cikin dan adam da kuma motsawar dattin ciki da yin bayan gida cikin sauki.



6. Amfani ga mata masu juna biyu

Wannan cimaka na kunshe da sinadaran minerals, da vitamins da kuma sauran abubuwan gina jiki da ke taka muhimmiyar rawa a lokacin da mace ke dauke da juna biyu.


Abubuwan da ke kunshe cikin yalo na taimaka wa mata masu juna biyu da jariran da ke cikinsu wajen kasasncewa cikin koshin lafiya.


Suna kuma kunshe da sinadarin folic acid wanda ke da amfani ga masu juna biyu. Folic acid na bayar da kariya ga jarirai daga samun wata tawaya ta wasu lokuta kan faru.



7. Bayar da kariya daga matsalar karancin jini

Masana sun gano cewa yalo ka iya zama wani magani na warkar da cututtuka kamar na numfashi, da kumburin ciki, da ciwon kai, da sauran su idan ana ci a ko da yaushe.


Yalo kan taimaka wajen kara yawan kwayoyin halittar jini a jiki, don haka yana yaki da matsalolin da ke haddasa karancin jini ko kuma sinadarin iron.


Yana kuma kunshe da sinadaran copper, tare da taimakawa wajen inganta kara yawan zagayawar kwayoyin halittar jini sosai ta hanyar jijiyoyin jinin dan adam, don haka yana kara karfi da kuzari.



8. Kariya daga kamuwa da ciwon suga (Diabetes)

Ta bangaren ciwon suga ko kuma diabetes kuma, yalo na taimakawa wajen bayar da kariya saboda yana kunshe da sinadarin fibre mai saurin narkewa da kuma carbohydrates da kan shi ma kan taimaka.


Na'ukan abinci masu kunshe da fibre da carbohydrates na taimakawa wajen tantance yanayin tsotsewar suga da bulkodin jini.


Abinci ne mai kyau ga masu fama da ciwon suga, saboda yana ragewa tare da bayar da kariya daga kamuwa daga cutar suga ko diabetes mataki na 2.



9. Daidaita hawan jini (BP) da kitsen cikin jini (cholesterol)

Har ila yau yalo na kunshe da sinadarai minerals masu yawa na calcium, da magnesium, da potassium, da kuma phosphorus da ke taimakawa wajen daidaita ayyukan kwayoyin halitta da sinadaran jiki a cikin jiki, don haka yana daidaita yanayin adadin karfin zagayawar jini wanda ke bayar da kariya daga cutar hawan jini.


Don haka yawan cin yalo na taimakawa wajen daidata karfin hawa da saukar jini da kuma kitsen cikin jinin.



10. Bayar da kariya daga cututtukan zuciya

Ta bangaren cutattukan da ke shafar zuciya kuma, yalo wanda ke kunshe da sinadaran vitamin B1 da B6 (thiamine da niacin).


Wadannan sinadarai na vitamins na da muhimmanci a cikin jiki wajen ayyukan zuciya da kuma fitar da zufar jiki.


Suna kuma kunshe da sinadarin potassium da ke taimakawa wajen daidaita karfin aikin jinin jiki.


Gargadi

🍠 Gargadi da shawarar masana game da cin yalon da ya wuce kima

Duk da irin dumbin amfanin da aka bayyana cewa yalo na da shi ga lafiyar jikin dan adam, akwai kuma gargadi da masana ke yi na matsalolin da ka iya faruwa idan aka rika cin yalon da ya wuce kima.


Don haka yana da kyau idan za a ci yalo a rika ci daidai gwargwado don kaucewa matsalolin da ka iya biyo baya cin shi da yawa.


Bai kamata mace mai juna biyu ta ci yalon a ko da yaushe ba saboda yana kunshe da sinadarin da ke kara saukar da jinin haila.


Yawan cin yalo ka iya haifar da matsalolin da yawan sinadarai masu kunshe da sinadarin potassium mai yawan da ka iya haifar da matsaloli idan suka yi yawa.


Yawan sinadarin potassium ka iya haifar da amai, da rudewar ciki, da yawan sinadari fibre da ka iya haifar da gudawa, har ma da matsalar rashin narkewar abinci mai gina jiki a kan kari Yalo na cikin dangin nau'ukan abinci da ke haddasa tashin zuciya, da kaikayin jiki, da kumburin makogwar.

Comments