Main menu

Pages

FALALAR TAIMAKON MARAYU DA AMFANINSA CIKIN AL'UMMAH

 



Falalar dake cikin taimakon Marayu da Alfanunsa cikin Al'ummah.


Daga:

Mal. Dayyabu Umar Memai Rano. 

 

Malamai sun fahimci cewa temakawa marayu yana cikin dalilin da yake kawo zaman lafiya a tsakanin al'umma. Misali: Duk wanda idan yaga anyi mutuwa marayun da aka bari suna samun kulawar gaske daga al'umar Annabi (ﷺ), to bazeji tsoron mutuwa ba akan daukaka addinin Allah. 



Bugu da kari baze sace kudin al'uma dan tarawa 'ya'yansa ba dan yaga yadda marayu suke samun kulawa, kaga kenan masu sace kudin jama'a saboda su barwa 'ya'yansu zasu ragu, masu kin ciyar da dukiyarsu su taskacewa 'ya'yansu zasu ragu wanda hakan ze temaka sosai wajen rage wadanda zasu zama 'yan wuta saboda wadannan matakai da al'uma suke dauka na kulawa da marayu. 

Comments