Main menu

Pages

JARUMAN KANNYWOOD BIYU DAKE CIKIN MAWUYACIN HALI, SUNA NEMAN ADDU'A

 Jaruman Kannywood biyu dake cikin Wani Hali suke bar Addu'arku.

Umar Yahya Bankaura da Haj Ladidi Fage na neman Addu'sr ku bisa rashin Lafiyar da suke ta fama da ita.Idan aka duba za aga yadda Haj Ladidi yanayi ya canja saboda rashin lafii da take fama da ita a wannan lokaci, Wanda ta dade da wannan jinya Muna Mata fatan samun Lafiya.
 Haka shima Kuma wannan tsohon ɗan wasan kwaikwayon nan Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) ya bayyana cewa ya na buƙatar addu’a daga al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala a jihar Kano, inda ya ke kwance magashiyan.
Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Ka-Fi-Gwamna saboda rol ɗin sa a diramar ‘Kwana Casa’in’ ta gidan talbijin na Arewa24, ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a assasa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.Mai shirya mujallar film ne ya Kai ma Alh Yakubu kafin Gwamna ziyara a asibiti, Wanda saboda tsananin halin da rashin Lafiyar yake ciki ya kasa gane Alh Umar din. Inda shi Kafi - Gwamnan yake shaida mashi tun karamar sallah yake kwance Yana jinya.
Sannan ya Kara da cewa kazo a lokacin da bazan iyayi magana sosai ba, kaima dai kaga halin da Nike ciki. Don haka a fada ma mutane su Sanya shi cikin addui.Kuma dai kunga ga a yadda suke. Kuma suna fatan ku ci gaba da yi musu addu’a; Allah ya Basu lfy tare da sauran Yan uwa Dake kwance ba lafiya a wannan lokaci.”

Ga hotunan su kuga yadda suka koma.

Alh Umar Malumfashi (Kafi - Gwamna)Haj Ladidi Fagge (Jarumar Finafinai)


Hajiya Ladidi Fagge


Comments