Main menu

Pages

YANDA AKE SOFT PEANUT AND COCONUT BALLS

 Yadda ake soft peanut and coconut balls


Barkanmu da sake haduwa a fanninmu na girke-girke.

A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake soft peanut and coconut balls.


Abubuwan hadawa;

Gyada kofi1

Kwakwa kofi ½

Sugar kofi ¾

Madara ta gari cokali 3 babba

Man gyada ko butter cokali 1

Ruwa cokali 1


Yadda ake hadawa

Ki gyara gyadan ki kidan cire bawon jikin, sai ki daka a turmi sama sama, ajiye a gefe.


Dauko kwakwa ki cire bakin jikin, sai ki gurza shi a jikin abun goge kubewa, say ki ajiye a gefe.


Ki daura non stick pan naki akan wuta (ki rage wutan) ki sa sugar sai ki na juyawa a hankali har sai sugar ya narke.


Sai ki kawo ruwa ki sa ki juya, ki kawo man gyada ki sa ki juya sai ki dauko gyada ki zuba ki kawo kwakwa ki sa ki juya, sai ki kawo madara ki sa ki juya ki kashe wutanki.


Ki shafa mai a jikin faranti sai ki juye hadin ki ki yi rolling na shi, sai ki na diban kadan kadan ki na mulmula da tafin hannu ki. A ci dadi lafiya.

Comments