Main menu

Pages

YA AJIYE AIKIN COMPANY SABODA ANA HANA SHI SALLAH A LAGOS

 Matashi ya ajiye aikin company saboda ana Hana shi yin sallah kan lokacinta


Assalamu alaikum Warahmatullah

Wani matashi mai suna Abdullahi Sulaiman da aka fi sani da Rt Hon Abulali Kankara ya ce ya jingine aikin wani kamfanin mai da ke birnin Lagos domin hukumomin kamfanin na hana shi yin sallah a duk lokacin da zai yi.


Matashin dan asalin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina ya ce yana aikin da kamfanin mai na Nest Oil Lagos, amma matsalar da ya samu da kamfanin shi ne, duk lokacin da ya bukaci zuwa ya yi sallah, sai manyansa su hana, su ce masa ya bari sai an tashi aiki, sannan ya hade duka ya yi.A wata ganawa ta musamman da matashin ya yi da DCL Hausa, ya shaida mata cewa hukumomin kamfanin sun ce masa ai bai fi sauran musulmai ba, don haka ya yi hakuri idan zai iya, idan bai iyawa kuma ga hanya nan.Aiki ne nake yi a wani kamfanin mai na Nest oil a nan Lagos. So duk lokacin dana nemi su bani dama na je na yi sallah sai su ce a'a, wai dole sai dai idan na tashi gaba daya kana na je na yi. So, ni kuma gaskiya ba zan iya hakan ba saboda neman duniya na saba da Ubangijina.Shi ya sa na yi ‘deciding’ na a je musu aikin su gaba daya. Akwai wani dan Maiduguri da muka hadu da shi ce mani ya yi “Rabon da ya yi sallar Juma’a, tun kafin ya fara aiki kamfanin! Karshe fa shi chief security na kamfanin da muka yi magana da shi ce mani wai ni na fi sauran musulman da ke wurin ne? Su sun hakura sun dai na sallar Juma’ar, khamsus salawatin ma sai dai idan sun tashi kana su hada gaba daya, so ni kuma ba zan iya hakan ba, shi ya sa kawai na hakura da aikin. Inji shi”.


To muna fatan Wanda ka ajiye aikin domin Shi, Ya canza maka da aiki Mafi Alkhairi fiye da wanda ka baro. Allah Ya tabbatar da imaninka har karshen rayuwarka. Ameen.

Comments