Main menu

Pages

TA KASHE MIJINTA SAURA KWANA 7 A KAWO MATA KISHIYA

 Ta kashe Mijinta ana Sauran kwana 7 a kawo mata Amarya.


Assalamu alaikum Warahmatullah

A wayewar safiyar yau mun samu wani mumunan labari da babu dadin ji inda wata mata ta hallaka mijinta saboda tsananin kishi irin na mata na hauka da jahilci.Datti assalafy ne ya ruwaito wannan labarin a shafinsa na sada zumunta inda al’amarin ya faru a jihar birnin kebbin da ke arewa maso yamma.


Wannan bawan Allah Lauya ne, sunansa Barr Attahiru Ibrahim Zagga daga jihar Kebbi, yana da mata amma sun rabu sakamakon bakin kishi na jahilci da ta tayar saboda yana shirin kara aureYau saura kwana 7 a daura masa aure da sabuwar amaryansa da zai aura a Maiduguri, to sai shekaran jiya matarsa da suka rabu ta nemo ‘yan ta’adda suka tafi gidansa suka rutsashi, suka dinga caccaka masa wuka har sai da hanjin cikinsa ya fito
Yan ta’addan sun samu nasaran tserewa, amma ita matar an kamata kafin ta tsere, yanzu haka tana State CID na jihar Kebbi


Zaku ga gashi har da invitation card dinsa zai kara aure, tsohuwar matarsa ta kashe shi saboda laifinsa kawai zai kara aure bata so


Muna fatan Allah Ya jikan Barr Attahiru, Allah Ya tona asirin duk wanda yake da hannu a kashe shi”

Comments