Main menu

Pages

HUKUNCIN DA RUNDUNAR SOJOJI TA YANKEWA MAKASAN SHEIKH GWANI AISAM

 Hukuncin da Rundunar sojoji ta yankewa makasan Sheikh Gwani Aisam.


Assalamu alaikum Warahmatullah.

Rundinar sojin Nigeria ta kori sojoji guda biyu wadanda ‘yan sanda suka kama da laifin aikata kisan kai, fashi da makamiSune sojojin da suka harbe babban Malamin Musulunci a jihar Yobe Sheikh Muhammad Goni Aisami tare da yunkurin sace motar Malamin Datti Assalafy ya ruwaito.
Sojojin masu mukamin Lance Corporals wato Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Gideon Adamu, amma kafin a koresu daga aiki sai da aka rage musu matsayi zuwa kuratan Sojoji wato PrivateLaftanar Kanar Ibrahim Abdullahi Osabo shine Mukaddashin Kwamandan Recce Battalion rundina ta 241 dake da sansani a garin Nguru jihar Yobe inda sojojin suke aiki ya gabatar da korarrun sojojin, sannan ya mikasu wa ‘yan sanda domin a gurfanar da su a Kotu
Aladu sun kashe ragon layya, tabbas ba zasu tsira ba

Muna fatan Allah Ya tabbatar musu da mafi tsananin hukunci

Allah Ya karbi shahadar Sheikh Muhammad Goni Aisami.

Comments