Main menu

Pages

UQUBA BIYAR DA KE JIRAN KOWANE MUSULMI

 Ukuba biyar da ke jiran kowane Musulmi. Inji Annabi saw.


Assalamu alaikum Warahmatullah.
A yau mun zo da tunatarwa akan wasu abubuwa biyar dake jiran Musulmi.

ANNABI (S.AW) YACE AKWAI UQUBA GUDA BIYAR WANDA DUK MUSULMI SAI YA HADU DA ITA. Wadannan abubuwa kuwa sune kamar haka;

 1. Mutuwa da dacin fitan rai.

 2. Kwanciyar kabari da duhun sa.

 3. Tambayar kabari da tsananin sa.

 4. Hawan siradi da santsin sa.

 5. Awon mizani da qididdige shi.


 SAI SAYYIDINA ABUBAKAR YACE: YA RASULILLAH MENENE ZAI IYA KAREMU DAGA WADANNAN ABUBUWA GUDA BIYAR ?

 SAI ANNABI (صلى الله عليه وسلم) YA CE:

 1. Sallar Asubah cikin jam'i yana hana jin dacin mutuwa.


2. Wanda ya yi sallar Azuhur cikin jam'i za a buda kabarinsa da haske.


3. Wanda yayi sallar Asri cikin jam'i za a saukake masa tambayar kabari.


4. Wanda ya yi sallar Magriba za a saukake masa hawan Siradi da santsin sa.


5. Wanda yayi sallar isha'i cikin jam'i za a saukake masa awon Mizani da qididdigeshi.


WANNAN SHINE KARIYAR DA ANNABI (صلى الله عليه وسلم) YABAMU.


 ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMAR SA.


Share to All Your contact

Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Comments