Main menu

Pages

TOFA! TA YIWA KANTA ALLURAN JININ SAURAYINTA MAI HIV

 Budurwa tayiwa kanta Alluran JININ da ke dauke da cutar kanjamau.

Wata budurwa ‘yar shekara 15 a yankin Sualkuchi, da ke birnin Assam na kasar Indiya ta yi wa kanta allurar jinin da ke dauke da cutar kanjamau na saurayinta, a jikinta bisa dalilin zurfafawa, gami da nuna soyayyar gaskiya a gareshi. Shafin Labarunhausa na ruwaitoYadda budurwar ta hadu da masoyin nata

Rahotanni sun bayyana cewa, matashiyar ta hadu da saurayin nata ne ta hanyar Facebook. Daga nan sai ƙaunar juna ta ƙaru a tsakanin su, a sakamakon hirar da suke yi akai-akai wadda ta sanya suka kara shakuwa, ta yadda suke jin cewa daya bazai iya rayuwa ba idan babu dayaBudurwar ta yiwa kanta allurar jinin masoyin na ta mai dauke da cutar kanjamau domin kada a raba su

A cewar gidan talabijin na Kalinga, masoyan sun kasance tare tsawon shekaru uku da suka wuce kafin yarinyar ta dauki wannan matsanancin matakin.A can baya budurwar tayi yunkurin guduwa da saurayin

An ruwaito cewa, yarinyar ta kuma yi kokarin guduwa da masoyinta sau da dama a baya, amma iyayenta suna dawo da ita gida. Amma wannan danyen aiki da budurwar ta yi a wannan karon sam babu wani daga yan uwan ta ko kewaye da ya taba tsammanin kasancewar sa.Ta yiwa kanta allurar jini mai cutar kanjamau

Yarinyar ta yi wa kanta allurar jinin da aka dauka daga wurin masoyinta mai cutar kanjamau, ta hanyar amfani da sirinji. Bayan yan uwanta sun sami labarin wannan lamari mai ban mamaki, sai suka yi karar masoyin nata a gaban shari’a .Yanzu haka ‘yan sanda sun tsare saurayin nata, yayin da ita kuma take karkashin kulawar likitoci


Bayan bullar wannan labari, Jama’a sun yi mamakin ganin yadda matasan kasar ke yanke irin wadannan matakai da ba su dace ba, gami da barazana ga rayuwa

Comments