Main menu

Pages

FATI WASHA TA RIKE NI MUN SHIGA ALJANNAH CEWAR WANI JARUMI

 



Fati Washa ta rike ni Mun shiga Aljannah, cewar Wani Jarumi, Amma fa a mafarki

Assalamu alaikum WarahmatullahWani

 Matashi Yayi Mafarki Fati Washa Ta Kama Hannunsa Sun Shiga Aljannah,  Ya Bayyana Yadda Mafarkin Nashi Ya Kasance;


KAJI RABO: Na Yi Mafarki Fati Washa Ta Riƙe Hannuna Mun Shiga #Aljanna, Inji Sabon Jarumin Kannywood Zeek Ilela



Sabon jurumi a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Auwal Abdullahi Zeek Ilela ya bayyana cewa wata rana ya yi mafarki jaruma Fati Washa ta riƙe hannunsa sun shiga Aljanna a Lahira.



Jarumi Auwal ya ƙara da cewa wannan shi ne babban dalilinsa na shiga harkar fina-finan Hausa saboda ya tabbatar akwai alkhairi a cikin mafarkin tunda ya haɗu da Fati Washa.



“Na daɗe ina son Fati Washa domin mace ce mai ƙira da cikar halittar macentaka, wata rana na yi mafarki mun haɗu da ita a lahira, ga ƴan uwana da abokaina da sauran mutane amma ita ce ta kama hannuna mu ka shiga gidan aljannah tare, shi isa na yi sauri na shiga cikin harkar fim domin mu haɗu tare tun a duniya tayadda mafarkina zai zama gaskiya a ranar lahira,”. Inji shi.



Auwal Abdullahi ya cigaba da cewa bai san haka ƴan fim su ke da kirki ba sai da ya shiga cikinsu saboda haka mutane su na yi musu gurguwar fahimta ne a rayuwa ta zahiri amma a baɗili su ɗin mutanen kirki ne, “a daina yi wa ƴan fim mummunar fassara domin mutanen kirki ne,”. Inji Sabon Jarumin na Kannywood Zeek Ilela.

Comments