Main menu

Pages

MAGANIN KURAJEN FUSKA (PIMPLES) DA TABO (DARK SPOTS)

 Yadda Zaki magance kurajen fuskarki da tabbai

Assalamu alaikum Warahmatullah.

Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza.

Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.

         Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya, duk yadda kika so ki gyara fuskanki make up dinki ya fito idan akwai pimples ko spots to abin baya armashi. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.


Da yawan mutane sun gwada mayukan kanti, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi ba.


To a yau Insha Allah  mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da zamu lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne, garin neman gira a rasa Ido.


- Da farko za a samu ganyen dogon-yaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi. Ayi ta yin hakan har sai kurajen da tabban sun bace.


· Za a samu dankalin turawa a markadashi, idan kina da blender zaifi miki sauki, sai ki blending ki ringa shafawa a fuska. Dankalin turawa na gyara fuska sosai, ba iya kashe kurajen da batar da tabo ba. Yana sa fuskarki ta dinga glowing tayi fresh, Kuma yana sa ki looking younger than your age.·- A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan tana magance tabon fuska.


- A hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.


· A samu hodar ‘baking soda, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi. A kula, baking soda ba baking powder ba.


Wanda keson rarrabewa tsakanin baking soda da baking powder ya duba a website din an akwai post akan banbancinsu, Kuma da yadda kwali ko gwangwanin kowacce yake.

    Allah yasa mudace da Alkhairi Ameen.

Comments