Main menu

Pages

KOTU NA KOKARIN DANNE HAKKIN FATIMA DA AKA CIRE MA KAFA

 Yanda Kotu ke kokarin danne hakkin Fatima yarinyar da aka buge har ya Kai ga yanke mata kafa.


Assalamu alaikum Warahmatullah

A yau ne ranar zaman case din Fatima a kotu,  yarinyar da Wani yaro ya buge ranar da suka gama jarabawar Neco a Sokoto. Inda matsalar ta kai har aka yanke mata kafa daya.  To a yau dinne Ake zaman sharia'ar, inda Alkalin kotu yaki halartar kotun kwatakwata.Yayinda kuma aka hana 'yan jarida daukar rahoton rashin zuwa wajen kamar yadda wani mai suna Jalaludeen Aliyu Ya ruwaito a shafisa na facebook yana cewa."Fatima yarinyar da wani Yaro ya buge da mota sai da aka cire mata kafa , yau 29 August an zo court.


Brother Fatima yake gaya min Alkali bai zo ba, kuma an hanama yan jarida dauka , kamar dai ana so a canza labarin nan.

Allah ya kyauta…


Justice for Fateema”

Ga video da muka dauko daga Facebook yadda ta kasance tsakanin Jami'an tsaro da Kuma masu daukar rahoto.
Comments