Main menu

Pages

FALALAR AZUMIN RANAR ALHAMIS DA LITININ
Falalar Azumtar ranar Alhamis da Litinin


Assalamu alaikum Warahmatullah

 Na farko dai manzon Allah saw ya sunnatar da wannan Azumin a Rayuwar sa Har ya Koma Ga Allah. Kunga kenan Sunnah Ne yin Wadannan Azumin. Na biyu kuma manzon Allah saw yana yin Azumin litinin ne Sabida a Ranar ne aka Haife shi. Sai yace shiyasa Nake Yin Azumin Ranar Litnin. Sabida Murna da Ranar da Aka Haifeni, Murna da Ranar da Na zo Duniya. Wannan kenan ya nuna Mana cewar duk wanda zaiyi koyi da Manzon Allah saw Azumi Zai dinga yi a duk Ranar Litinin. Kamar yadda Haka yake yi har Ya Bar Duniya, s.a.w Haka zalika an tambayi Manzon Allah saw Akan Azumin Ranar Alhamis da yake yi. Sai Yace Ina Yin Azumi a Ranar Alhamis Ne, Sabida a duk Ranar Alhalin Ne Ake Tattara ayyukan Bayi Na Sati guda a tafi Sama Dasu ya Zuwa ga Allahu Subhanahu Wata'ala. Shiyasa Nake yin Azumi duk Ranar Alhamis Domin a tafi da Ibada ta na wannan satin Alhalin Ina Yin Azumi. Sannan Kuma Manzon Allah saw Yace, Ladan Azumi Allah ne da kanSa yake Rubuta shi. Saboda Tsabar yawan Ladan Wannan Azumin Allah bai wakilta wani Mala'ika ya Rubuta shi ba. Ubangiji Allahu Subhanahu Wata'ala da Kansa yake Rubuta Ladan Mai Azumi. Sannan Manzon Allah saw Yace Duk wanda yayi Azumi guda daya Saboda Allah, Allah zai Nisantar da Fuskarsa daga shiga Wuta Na Tsawon Tafiyar Shekara Dari Biyar.  Saboda Haka, Duk wanda Allah ya Bashi Iko. Sai ya Kula da yin Wadannan Azumummuka Guda biyu. Saboda Neman Dacewa a Ranar Tonon Asiri. Domin Manzon Allah saw Yace a Cikin Aljannah Akwai Wata Kofa da Ake Cewa AR-RAYYAN Babu Mai shiga ta Cikinta Sai Mai Azumi.  Allah Da Kansa zai Kira Masu Azumi, Zai ce INA MASU AZUMI? Zasu ce Gamu ya Allah. Sai Allah Yace da su KU SHIGA TA WANNAN KOFAR.  Sannan Manzon Allah saw Yace AZUMI ZAI YI CETO A RANAR ALKIYAMA. ZAI CE YA UBANGIJI, INA NEMAN CETON WANNAN BAWA NAKA. YA BAR CI DA SHA DUK SABODA KAI. SAI ALLAH YACE AN BAKA CETON SA. Allah Ya sa Mu cika da Imani.

 Saboda haka Sai Mu Daura Niyya. Daman dai kowa ya san bauta ta kawo mu wannan duniya. Saboda haka wanda yake da Iko sai ya dage. Allah Ya bamu iko gaba dayan mu

Comments