Main menu

Pages

ALI ARTWORK YASHA DUKA WAJEN JAMI'AN DSS DA SHANYA SHI A RANA

Yadda DSS suka lakadawa Ali Artwork dukan tsiya a kaduna


Yau din nan muke samun wani labarin yadda jami’an Dss suka yiwa Ali Artwork Madagwal dukan tsiya suka shanya shi Kuma a rana, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram kamar haka;
YAU A GARIN KADUNA JAMI AN DSS NA KADUNA SUNYIWA SHAHARARREN ME WASAN BARKWANCI WATO ALI ARTWORK MADAGWAL DUKA DA SASHI YA KALLI RANA SABODA YA KAWO KOKEN SA A KAN WASU MATSAFA DAKE BIBIYAR RAYUWARSA DA TA DAN UWANSA DAYAKE AIKI A WANNAN MA’AIKATA DSS YA SHIGAR DA KOKEN TUN RANAR 9-6-2022 AMMA KULLUM YAZO BABU AMSA MAI DADI YANZU HAKA DAN UWAN NASA YANA NAN RAI A HANNUN ALLAH BAYAN ALI ARTWORK MADAGWAL YA NEMI A MUSU ADALCI AKA KI SHINE DA YA FUSATA YAYI MAGANA SHINE SUKACE WAI YAYI MUSU RASHIN KUNYA SHINE SUKA MAI DUKA SUKA KORESHI DAGA WAJEN DA SHI DA DAN UWAN NASA SANNAN SUKACE YA TAFI SHI ZAI KULA DA DAN UWANNASA SU BABU RUWANSU A SANI MU BABAN MU SHUGABAN DSS NA KASA MUTUMIN KIRKI NE KUMA BAYA SON ZALINCI AMMA AN SAMU WASU DAGA CIKIN GURBATATTUN MUTANEN DA KE AIKI A CIKIN WANNAN MA’AIKATA TA DSS SUNA SON SU BATA MASA SUNA DA AIKINSA BAYAN KUMA AIKINE DA YA SHIFI KARE AL’UMMAR KASA A SANIN TALAKAWAN KASARMU YANZU JAMI’AN DSS KAWAI SUKA RAGE A NIGERIA WANDA AKE MUSU KYAKYAWAN ZATO DA KULA DA AIKINSU YANDA YA
KAMATA SANNAN ANSAN MA’AIKATA BASA KARBAR CIN HANCI KO RASHAWA KO KWANAKI MA’AIKATA SUN GAYYACI A ALI ARTWORK MADAGWAL HAR GARIN ABUJA TA HANYAR DAN SHUGABAN DSS NA KASA WATO MUHAMMAD BICHI AKAN YA TAIMAKA MUSU WAJEN GANIN AIKINSU YA TAFI DAIDAI TA HANYAR SANA’AR SA TA BARKWANCI YAJE YA WAYAR DA KAN JAMA’A AKAN SHA’ANIN TSARON KASA KUMA YA YARDA ZAIYI BA TARE DA AN BASHI KO SISI BA BAI DUBA HALIN DA KASAR TAKE CIKI BA NA RASHIN TSARO AMMA YAJE YAYI VIDEO BA TARE DA YANA TSORON BASU AIKATA WANNAN LAIFI ZASU MASA WANI ABUBA SAI DAN YA DOGARA GA ALLAH SHINE MAI TSARE BAWANSA KUMA SHI ZAI TSARESHI DUK DUNIYA TAGA VIDEO DA YAYI A TASHAR MOTA
AKAN DIREBOBI BASU KARBAR SAKO BASU DUBA BA TA HANYAR HAKA AKAN IYA SAKA MAKAMAI A CIKI A KUMA KAISHI INDA baidace KUMA YA CUTAR DA Al’umma A DON HAKA NAKE ROKON BABAN MU ALH. MAGAJI YUSUF BICHI MUNA NEMAN ADALCI DAGA GAREKA A KULA DA CASE DINSU DOMIN ABUN ZAI TAIMAKI KASA DA AL’UMMAR KASAR MU NIGERIA DON KAUDA MIYAGU DAGA CIKIN AL’UMMAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W ALLAH YA TSARE MANA KASAR MU ALLAH YA TSARE MANA AL’UMMAR MU DARAJAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W.

 Ku  shiga wannan link din dake kasa don shiga account dinsa na Instagram inda ya wallafa abinda ya faru a cikin pages dinsa


Comments