Main menu

Pages

DALILIN DA YASA KAMFANIN WUTAR LANTARKIN NIGERIA KE YAJIN AIKI
Dalilin da yasa kamfanin wutar lantarki ke yajin aiki

 Ƴan Najeriya sun auka cikin duhu a wasu sassan ƙasar sakamakon tafiya yajin aikin da ma'aikatan wutar lantarki na ƙasar suka fara.


Sun fara yajin aikin ne ta hanyar hana shiga da fita a hedikwatar kamfanin dillancin wutar lantarkin na Najeriya TCN a Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da safe.


Sun fara kashe makunnan lantarki a ofisoshin da ke faɗin ƙasar.


Wani jami'in kamfanin ya shaida wa sashen BBC Pidgin cewa suna fatan gwamnati za ta shiga cikin lamarin, idan ba haka ba kuwa to kowa zai zauna a cikin duhu.


Yajin aikin ya samo asali ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma'aikatan Lantarkin da kuma Kamfanin Dillancin Lantarki na Najeriyar.


Abin da ya sa ma'aikatan TCN ke yajin aiki

Ƙungiyar ƙwadagon ta fara yajin aikin ne a ranar Laraba 17 ga Agustan 2022 don gwamnati ta saurari buƙatunsu.


Ma'aikatan kamfanin dillancin lantarkin dai na son a dakatar da tsarin aikin da ake bi na ci gaban ma’aikata.


Da umarnin da hukumar gudanarwar kamfanin dillancin lantarkin na Najeriya ta bayar ta yin jarrabawar ƙarin girma ga waɗanda suka kai muƙamin mukaddashin babban manaja da za su yi gaba zuwa muƙamin mataimakin Janar Manaja.


A daina nuna bambanci ko wariya ga ma’aikatan da suka fito daga ofishin shugaban ma’aikata na tarayya, wadanda ba a barinsu su yi aiki a wasu sassan bangaren samar da wutar lantarki.


Da gazawar kamfanin dillancin na samar da kudaden hakkokin da tsoffin ma’aikatan kamfanin samar da lantarki na kasar (PHCN) ya kamata a ba su.


Sun ce ba za su janye yajin aikin ba har sai gwamnati ta amsa buƙatunsu.Me gwamnati take yi kan yajin aikin?

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana tattaunawa da ƙungiyar ƙwadagon ƙasar don samo mafita ga ɗumbin matsalolin da suka jawo ma'aikatan lantarkin suka fara yajin aiki.


Ministan Lantarki Abubakar Aliyu ne ya sanar wa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa hakan, bayan kammala taron majalisar zartarwa da ake yi duk Laraba.


Ya ce batutuwan da ake taƙaddama a kansu na batun ɗaukar aiki ne da suke cikin hurumin shugaban ma'aikatan gwamnati na Najeriya ba ma'aikatar lantarki ba.


Jami'an kamfanin TCN sun shaida wa BBC Pidgin cewa "idan gwamnati ta gaza warware matsalar nan a yanzu zai shafi tattalin arzikin ƙasar kuma mutane za su shiga yanayi na sayen man janarero da shi ma aka ƙara masa farashi daga naira 165 zuwa sama da naira 170 a kan duk lita guda.


A shekarun 2000 ne gwamnati ta fara sayar da ɓangarorin hukumar samar da wutar lantarki.


Zuwa shekarar 2013 an sayar da kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 da kamfanonin samar lantarkin shida, yayin da gwamnatin ke ci gaba da iko da kamfanin dillancin lantarkin 100 bisa 100.


Amma cin hanci da rashin aikin yadda ya dace sun jawo cikas ga harkar.


Yawanci ana samar da wutar lantarkin Najeriya ne ta gas da ruwa da ke da damar da za a samar da megawat 12,522 na wuta.


Amma yawan lalacewar da babban layin lantarki na ƙsar ke yi tun farkon shekarar nan ya sa da ƙyar ake samar da megawat 4,000, abin da ke jawo ƙarancin wutar a ƙasar da ke da fiyte da mutum miliyan 200.


Yawan ɗauke wutar da ake yi ya tilasta wa ƴan Najeriya da dama, da sua haɗa da masu sana'o'i dogaro da man fetur don kunna janareto a gidaje da wuraren kasuwancinsu.


Tuni wasu kamfanonin lantarkin wasu jihohin suka fitar da sanarwa ga abokan hulɗarsu yadda yajin aikin zai shafe su.


To Amma dai abin bai he da nisa ba Allah Ya yadda sun janye yajin aikin.

Comments