Main menu

Pages

KO KUN SAN AMFANIN KHALL - TIFFA (APPLE CIDER VINEGAR)

 Amfanin khal - Tuffa (apple Cider vinegar)

Assalamu alaikum Warahmatullah

Yau za muyi bayani game da khal tuffa kadan daga cikin magungunan da yake yi,saboda da yawa mutane sun sanshi amma basu san amfanin da yake yi ba, Insha Allah ga wasu daga ciki.


1. Ana amfani da shi wajen wanke gashi yana sa kyalli, yana qara ma jijiyoyin kai kwari yana sa gashi tsayi tareda kashe dandruff cikin kan kanin lokaci.


2. Yana maganin dattin haqora a dangwalo kadan a goge haqora da shi sai a kuskure dà ruwa.


Yana maganin sunburn, discoloration, ariqa zubawa cikin ruwan wanka ko ana goge wajen da aka san yana da matsalar. 


4. Ana amfani da shi wajen goge hammata after shaving yana hana kuraje fitowa, yana sa haske.


5. Ana amfani da shi wajen rage kiba ko tumbi, ana zuba 2 teaspoons a ruwa asha early in the morning and night.


6. Shan khal tuffa na taimakawa wajen wajen matsalan hawan jini.


7. Shan shi na taimakawa kwarai wajen rage yaduwar cutar yeast infections wadda tafi kama mata.


8. Ana amfani da shi wajen wanke bayi, kwanu ka, flour, tiles yana kashe bacterium, yana sa haske.


9. Ana amfani da shi wajen kashe kwari a gida, azuba a abin feshi ayi spraying.


10. Yana maganin dandruff a zuba abin feshi ayi spraying a kai a barshi .


11. Masu fama da skn problems irinsu pimples, rashes, spot, acne etc ayi dilutin sai a shafa a wajen.


12. Yana maganin matsalan rashin samun bacci idan ana hadawa da Zuma anasha kafin bacci da kuma bayan farkawa daga bacci.


13. Yana maganin matsalolin mafitsara( bladder) kasa yin fitsarin kokuma jin zafi lokacin yinta musamman masu bladder infection

Comments