Main menu

Pages

COMPANY MILK BOSTER TA KIRKIRO SABUWAR HANYAR SHAYAR DA JARIRAI MAMA.

  



Kamfani ta kirkiro matattara nono uwa don shayar da jarirai a Najeriya

Assalamu alaikum Warahmatullah

Kamfanin ‘Milk Booster’ ta kirkiro hanyar da za a rika shayar da jariran da uwayen su basu da ruwan nonon shayar da su a Najeriya.



Kamfanin ta kirkiro hanyar Samar wa wadannan jarirai nono ta hanyar samun ruwan nono daga uwayen dake shayarwa domin tallafawa jariran da basu samun ruwan nonon uwa.



Milk Booster ta kirkiro wannan hanya ne domin karfafa shayar da jarirai nonon uwa na akalla watanni shida.



Kamfanin ta gabatar da wannan dabara da ta kirkiro a makon shayarwa da ake yi daga ranar 1 zuwa 7 na kowani watan Agusta na kowace shekara.



Taken taron na bana shine inganta shayar da jarirai nono zalla ta hanyar wayar da ilimantar da mutane.



Shugaban kamfanin Dr Chinny Obinwanne -Ezewike ta ce kamfanin ta kirkoro wannan dabara ce domin kula da jariran da aka haifa ƙasa da wata 9, jariran dake fama da cuta da jariran dake fama da yunwa.



Obinwanne-Ezewike ta ce kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce a duk lokacin da aka haifi jaririn da mahaifiyarsa bata ruwan nonon da za ta shayar da shi kamata ya yi a nemi mace mai shayarwa da za ta shayar da jaririn ba a nemi madara a rika dura wa jariri.



Ta ce tun bayan kaddamar da Kamfanin shekaru biyar da suka gabata kamfanin ta taimaka wa jarirai sama da 50,000 a kasar nan.



Obinwanne-Ezewike ta ce shayar da jariri nono zalla hanya ce dake inganta garkuwar jiki da kare jariri daga kamuwa da cututtuka.



Bayan haka Obinwanne -Ezewike ta yi kira ga gwamnati da ta mara wa wannan kokari na su baya domin ganin har matan dake karkara sun amfana da shi.



“Zuwa yanzu kamfanin ta kashe sama da dala 165,000 domin ganin an tallafa wa jariran dake karkara.

Comments