Main menu

Pages

SIRRIKA 6 DAKE SA MATA SANYA JIGIDA - BINCIKEN MASANA

 


Sirrika 6 da saka jigida ke yi wa mace – Binciken Masana.

Assalamu alaikum Warahmatullah

Jigida wasu duwatsu kanana ne dake da nu’i daban daban da ake jera su a igiya ayi sarka da su ana sakawa a kwankwaso domin kwaliya.


Wannan irin kwaliyan ya fi suna a wurin matan yankin Nahiyar Afrika. Wasu kasashen har da maza ma sukan saka jigida.


Bisa ga al’adun gargajiya mutanen Afrika baya ga kwaliya akwai wasu dalilai da yasa suke saka jigida musamman matan su.


1. A wasu yankunan ana hada jigida mata su saka domin samun kariya daga iska ko mutanen boye, wato aljanu.


2. Wani jigidan akan haɗa da surkulle ne domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman kananan yara.


3. Wasu jigidan akan haɗa su mace ta saka a kwankwaso domin samun saukin naƙuda a lokaci haihuwa.


4. Akwai yakinin cewa saka Jigida na taimakawa wajen rage kiba musamman ga mata masu tumbi ko katon ciki.


5. Jigida na taimakawa wa mace wajen ƙara girman kugu wato Hips a Turance, dakuma samun farin jini cikin mutane


6. Jigida na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo sha’awa da ra’ayin namiji zuwa ga mace.


Sai dai kuma duk da wadannan kyawawan dalilan wasu mutane da dama basu son jigida saboda a ra’ayinsu jigida sarka ne da ake amfani da shi domin wani tsafi.


Wata mata da ta shahara a hada jigida Felicia Musa ta ce tana matukar sha’awar jigida musamman idan mace ta saka shi yana kara idan tana tafiya.


Ta ce jigida iri-iri ne akwai wanda wasu matan ke sakawa na farin jini ko na samun kariya amma yi hakan ba shine ke mai da mutum matsafi ba.


Felicia ta ce saka jigida ra’ayi ne idan kana so ka saka idan ba ka so ba za ka saka ba amma rashin son shi din ba shine zai ba mutum daman cusa wa mutane ra’ayin kin shi ko rashin son shi ba.

Comments